Bankuna Sun Fara Ba da Tsoffin Kudi, Amma Sun Sanya Iyakar Adadin da Za a Cire

Bankuna Sun Fara Ba da Tsoffin Kudi, Amma Sun Sanya Iyakar Adadin da Za a Cire

  • Bankunan Najeriya sun fara ba kwastomomi tsoffin takardun Naira bayan samun umarni daga CBN biyo bayan hukuncin kotun koli
  • Sai dai, duk da haka wasu bankunan sun gaza biyan bukatar kwastomomi, kasancewar suna fuskantar karancin kudi
  • A halin da ake ciki, bankuna sun sanya iyakar kudin da za a iya cirewa a kan kanta da kuma na’urorin ATM a kasar

Najeriya - ‘Yan Najeriya sun samu sauki yayin da bankunan kasar nan suka sanar da fara ba da takardun Naira tsofaffi a ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023.

Wannan na zuwa ne bayan da babban bankin CBN ya ba da umarni ga bankunan da su ci gaba da karba da biya da tsoffin N200, N500 da N1000 har zuwa karshen Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin Naira: Masu gidajen mai sun ki karbar tsoffin kudi duk da umarnin CBN, sun fadi dalili

Sai dai, binciken da Legit.ng ta yi ya nuna cewa, bankuna da yawa sun gaza biyan bukatun kwastomominsu saboda karancin kudin da suke fuskanta su kansu.

Bankuna da yawa da wakilinmu ya ziyarta a Legas, ciki har da wadanda ke Airport road, Ikotun da kuma na Ago Palace duk ba su da sabbi da tsoffin kudaden a kasa.

Bankuna sun fara ba da tsoffin Naira
Yadda karancin kudi ke jawo cece-kuce a Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yawan bankunan, kamar yadda aka yi tsammani, sun mayar da kudaden da suka karba daga hannun jama’a zuwa bankin CBN.

Saboda karancin kudi, bankuna da yawa sai suka sanya iyakar kudin da za a iya cirewa a kan kanta zuwa N20,000, sai kuma N10,000 a ATM.

‘Yan Najeriya sun tofa albarkacin bankinsu

Wani dan Najeriya mai asusu a bankin Zenith mai suna Damilola ya ce:

“A bankin GT da ke Obalande, ATM na iya ba da N10,000 na tsoffin kudi ga kwastomomin bankin yayin da wadanda basu da asusun GTB ke samun N1000."

Kara karanta wannan

Bayan Maganar Buhari, CBN Ya Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsoffin Naira N500 da N1000

Wata kuwa a Twitter, @MarAkinola cewa ta yi:

“Bana tunanin abubuwa za su koma yadda suke da a nan kusa saboda layi a GTB da safen nan ya kai mutum 510 kuma iya 4k kadai suke bayarwa na tsoffin kudi a kan kanta.
“Babu ATM da ke ba da kudi! Ina ga wannan lamarin ya fi karfin sauya fasalin Naira! Meye yasa ba za su ba da fiye da 4,000 ba?"

A daya daga bankunan Polaris da aka ziyarta, mai ba da kudi a kanta ya ce:

“Mun fara ba da N5,000 ga kowane kwastoma da safen nan, amma kudin ya kare da ranan nan. Za a samu karin kudi zuwa ranar Juma’a.”

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, bankin Wema da ke Town Planning Way a Legas na ba da N4,000 ta ATM ga kwastomomin da basu da asusu a bankin.

Masu asusu a bankin na samun N20,000 a ATM idan suka cire N10,000 sau biyu.

Kara karanta wannan

Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'

A bankin Access da ke bakin babbar kasuwa a jihar Gombe, ATM na ba da sabbin kudade da suka kai N10,000 ga kwastomominsa.

A kan kanta kuwa, ana ba da N20,000, amma duk da haka shiga bankin ya zama babban kalubale ga kwastomomi saboda tsananin layi.

Ya zuwa yanzu, wakilin Legit.ng Hausa ya zagaya bankuna sama da biyar a Commercial Area da ke Gombe, babu inda ake ba da tsoffin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.