Kaduna: Bayan Karbar Kudin Fansa N2m, Yan Bindiga Sun Sakin Mata, Miji Da Diyarsu
- Bayan karbar naira miliyan 2 a matsayin kudin fansarsu, yan bindiga sun ki sakin wasu ma’aurata da diyarsu a Kaduna
- Masu garkuwa da mutanen sun je har gidan mata da mijin da ke garin Janjala a yankin Kagarko ta jihar Kaduna sannan suka sace su
- Bayan miliyan biyu da suka karba, sun bukaci dangin wadanda aka sacen da su kawo masu sabon babur kafin su basu yanci
Yan Bindiga sun ci gaba da tsare wasu iyali uku da suka yi garkuwa da su duk da cewar sun karbi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansarsu daga wajen yan uwansu a garin Janjala da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga sun kai farmaki gidan ma’auratan a Janjala sannan suka yi awon gaba da Mista Mustapha Da Matarsa, Malama Shamsiya da diyarsu yar shekara 16, Mahapuza.
Yan bindigar sun nemi a sake kawo sabuwar babur kafin su sake su
Wani dan uwan mutanen da aka sace, Garba Dayyabu, wanda ya zanta da jaridar ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce an kaiwa shugaban yan bindigar kudin fansa a dajin da ke kewayen Kududdufin Kachia a ranar Juma’a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce bayan ya karbi naira miliyan 2 shugaban yan bindigar ya ce su je su kawo sabuwar babur kafin a saki mutanen.
Madakin Janjala, Samaila Babangida, wanda ya tabbatar da ci gaban, ya ce:
“An fada mani cewa yan bindigar na neman a kawo masu sabuwar babur bayan N2m da aka basu kafin su saki mutanen.”
Martanin yan sanda
Har yanzu ba a samu jin ta bakin Kakakin yan sandan jihar Kaduna ba a kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton, Platinum Post ta rahoto.
Yan bindiga sun farmaki Zamfara sun kashe DPO da wasu 2
A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa yan bindiga sun kai kazamin hari hedkwatar karamar hukumar Maru ta jihar Katsina inda suka kashe wani shugaban yan sanda na yanki, DPO da wasu jami'an tsaro biyu.
Wannan al'amari ya haifar da tashin hankali a tsakanin al'ummar yankin yayin da suka tsere don neman mafaka.
Asali: Legit.ng