Na Kashe Mutane Sama Da 15 A Katsina Amma Ina Neman Afuwa, Ɗan Ta'adda Mai Shekaru 28 Da Dubunsa Ta Cika
- Wani mashahurin dan fashin daji ya shiga hannun jami'an yan sanda biyo bayan zarginsa da laifuka daban daban
- Yar bushiya mai shekaru 28 ya bayyana cewa ya kashe sama da mutane 15 a hare hare daban-daban da aka kai da shi
- Dan fashin dajin ya roki da a masa afuwa tare da alkawarin ba zai sake aikata laifin ba idan aka yafe masa
Katsina - Wani dan shekaru 28, Sulaiman Iliyasu na Walawa Asaurara, Sabuwar Unguwa, karamar hukumar Jibiia, da ke Jihar Katsina ya bayyana cewa ya kashe sama da mutane 15 a hare haren yan bindiga daban-daban a fadin Jihar Katsina.
Iliyasu, wanda aka fi sani da Yar bushiya ya bayyana haka ne a hedikwatar yan sanda ta Jihar Katsina inda aka gabatar da shi a gaban yan jarida ranar Talata, Vanguard ta rahoto.
An Kama Bokan Da Ke Yi Wa Mutane Alkawarin 'Azirta' Su Ba Tare Da Amfani Da Sassan Jikin Dan Adam Ba A Edo
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya gabatar da wanda ake zargin ya bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
''Yar bushiya ya shiga hannun jami'an yan sanda, da ke Dutsinma a kwanakin baya bisa zargin manya laifukan da suka shafi ta'addanci."
Gambo ya cigaba da cewa:
''Wanda ake zargin ya gudanar da ayyuka da dama da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma satar shanu a fadin jihar."
Na zauna a sansanin Dankarami, In Ji Yar Bushiya
Yar bushiya ya sake bayyana cewa ya yi aiki a tawagar ''Dankarami,'' wani shahararren jagoran yan ta'adda, da yan sanda ke nema ruwa a jallo bisa aikata laifuka da suka saba da doka a jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna, Kebbi da kuma Sokoto.
Wanda ake zargin ya kuma shaida cewa ya sha shiga ayyukan yan fashin daji tsahon shekaru uku da suka gabata wanda aka kai hari da shi a Sabuwar Dandume, Faskari, Jibia, Batsari, da kuma Kurfi a Jihar Katsina.
Idan an yafe min ba zan sake komawa daji ba, Yar Bushiya
Yar bushiya ya roki da ayi masa afuwa tare da alkawarin ba zai sake aikata laifin ba idan aka yafe masa.
Asali: Legit.ng