Ganduje Ya Jajantawa Yan Kasuwar Kano Da Gobara Ya Shafa
- Gwamna Ganduje na Jihar Kano ya mika sakon jaje ga yan kasuwannin Rimi, Kurmi da Singer da iftila'in gobara ya afkawa a kwanakin nan
- Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya rabawa manema labarai a jihar
- Ganduje, ta bakin Anwar, ya kuma bada tabbacin cewa ana cigaba da bincike don gano musabbabin gobarar da ta addabi kasuwannin a baya bayan nan
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jajantawa yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwannin Kurmi, Rimi da kuma Singer a Jihar.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya raba wa yan jarida ranar Talata 14 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gobarar ta lalata kadarori na miliyoyin kudi.
Da ya ke adduar Allah ya baiwa yan kasuwar hakurin jure asarar da yan kasuwar suka yi, Ganduje ya bukaci wanda abin ya shafa da su dinga dubawa suna kuma tabbatarwa sun kashe kayan amfanin lantarki kafin barin wuraren kasuwancin su.
''A madadin gwamnati da mutanen Jihar Kano, ina mika sakon jajenmu ga wanda suka rasa dukiyoyinsu. Allah ya mayar mu su da alheri anan gaba.
''Wannan abin a tausaya ne ba iya ga masu shaguna ba, ya shafi dukkan mu. A takaice duk kasar nan ya shafa. Allah ya basu ikon yadda da haka a matsayin kaddara daga ubangiji'' kamar yadda Anwar ya rubuta jawabin Ganduje a sanarwar.
Ya bayyana cewa ana cigaba da bincike daga tushe don gano musabbabin gobarar.
Mummunan gobara ta yi barna, ta lakume shaguna 80 a kasuwar Kurmi na Jihar Kano
A wani rahoton a baya, kun ji cewa gobara ta tashi a kasuwar Kurmi a ranar Laraba 1 ga watan Maris na 2023 a Kano inda ta cinye a kalla shaguna 80.
Saminu Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na jihar Kano, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewarsa, hukumar ta kwana-kwana ta samu kiran daunan dauki daga wani Mallam Aliyu Alkasim misalin karfe 5.23 kan tashin gobarar.
Asali: Legit.ng