Gwamna Inuwa Ya Sha Jar Miya, ’Yan Takarar Gwamna 8 Sun Janye Daga Takara, Sun Bi Sahunsa

Gwamna Inuwa Ya Sha Jar Miya, ’Yan Takarar Gwamna 8 Sun Janye Daga Takara, Sun Bi Sahunsa

  • Gwamnan jihar Gombe ya kwashi jar miya, domin ‘yan takara takwas cikin 13 na gwamna a jiharsa sun janye kuma sun mara masa baya
  • Wannan na zuwa yayin da ya saura kwanaki uku kacal a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jiha a fadin kasar nan
  • Ya zuwa yanzu, manyan jam’iyyun da ke takarar gwamna a jihar sun hada da PDP, APC, LP da kuma NNPP mai kayan marmari

Jihar Gombe – Gabanin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya samu karuwa a fannin siyasarsa.

Gwamnan ya samu goyon bayan wasu jiga-jigai kuma ‘yan takarar gwamna daga jam’iyyun siyasa takwas a jihar ta Gombe, rahoton Leadership.

Shugaban gammayar jam’iyyun siyasa ta IPAC a jihar, wanda kuma dan takarar gwamna ne a jam’iyyar Zenith, Muhammad Gana Aliyu ya bayyana wannan batu na goyon baya ne ga manema labarai a jihar.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Takarar Gwamna 6 Sun Janye Daga Takara Kwana 5 Gabanin Zabe

Gwamna Yahaya ya samu goyon bayan jam'iyyun adawa
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewarsa, bayyana goyon bayan na zuwa ne bayan duba cikin tsanaki ga yadda gwamnan ya yi ayyukan ci gaba a mulkinsa cikin shekaru hudu kacal

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda suka janyewa Inuwa Yahaya baya a Gombe

Da yake jawabi, Aliyu ya bayyana wadanda suka marawa Inuwa baya kamar haka:

1. Muhammad Gana Aliyu na jam’iyyar ZLP

2. Sulaiman Abubakar Sunusi na jam’iyyar NRM

3. Sadiq Abdulhamid na jam’iyyar BP

4. Adamu Muhammad na jam’iyyar APP

5. Sulaiman Jibrin na jam’iyyar ADP

6. Adamu Aliyu Danmakka na jam’iyyar AAC

7. Kelmi Jacob Lazarus na jam’iyyar SDP

8. Muhammad Bello Abubakar na jam’iyyar APP

‘Yan siyasan takwas sun kuma yi kira ga magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwata domin dangwalawa Inuwa Yahaya kuri’unsu a zaben ranar Asabar mai zuwa, Tribune Online ta tattaro.

Wadannan ‘yan takara takwas da suka mika wuya da son ransu ga Inuwa suna cikin ‘yan takara 13 da suka sanya hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya da hukumar INEC, hukumomin tsaro da kungiyoyin farar hula suka gabatar a jihar a aranar 15 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

Dan takarar Labour ya bi Aisha Binani a Adamawa

A wani labarin kuma, kun ji yadda dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Labour ya bayyana janyewa daga takara tare da marawa Aisha Binani ta APC baya.

A cewarsa, ya fahimci akwai fahimtar juna da kamanceceniya a manufofin Binani da nasa a zaben na 2023 da ke tafe nan kusa.

Ya zuwa yanzu, jam’iyyun siyasa na ci gaba da musayar mambobi yayin da ake saura kwanaki kadna zaben gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.