‘Na Hango Matsala a Najeriya’: Fasto Ya Bukaci a Gaggauta Tsige Shugaban INEC Daga Kujerarsa

‘Na Hango Matsala a Najeriya’: Fasto Ya Bukaci a Gaggauta Tsige Shugaban INEC Daga Kujerarsa

  • Malamin coci a Najeriya ya bayyana irin matsalar da za a samu nan gaba kadan idan ba a tsige shugaban hukumar zabe ta INEC ba
  • Ya yi kira ga matasa da su yi hakuri, su fito su zabi wanda suke so a zaben gaba mai zuwa ranar 18 ga watan Maris dinnan
  • Malamin ya ce, Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya alkawarin tabbatar da zabe cikin lumana, don haka kada a tada hankali

Jihar Imo - Babban malamin addinin kirista, Rev Fr Magnus Ebere da aka fi sani da ‘E Dey Work’ ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta koran shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.

A cewarsa, matukar shugaban kasan na son Najeriya ta ci gaba da zama kasa mai kwanciyar hankali da zaman lafiya, dakatar da Yakubu ne mafita.

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

Ya bayyana hakan ne a gaban almajiransa da ke cocinsa na Cananland Adoration Counselling Centre, Mbaise da ke jihar Imo, Leadership ta ruwaito.

Magnus Ebere ya nemi a tsige shugaban INEC
Rev. Fr. Magnus Ebere kenan, fasto a jihar Imo | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Na hango matsala a Najeriya, cewar malamin coci

Malamin ya kuma bayyana cewa, yadda shugaban na INEC ya gudanar da zaben shugaban kasa, hakan zai iya jawo tashin hankali ga Najeriya idan ba a kula ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, ya ce dabi’un Yakubu a zaben shugaban kasa na bana zai iya tunzura ‘yan Najeriya da dama su fara tunanin kirkirar gangamin aware a nan gaba.

A cewarsa:

“Ina hango bayyanar kasashe da yawa masu tasowa daga cikin kasar nan idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a yadda suke yanzu.
“Abu mafi kyau da ya kamata a yi shine tsige shugaban INEC, Mahmud Yakubu, a soke zaben shugaban kasa sannan a sake sabo tare da sabon shugaban da zai kula da zaben.”

Kara karanta wannan

Tinuba ba zabin Allah bane: Dan takarar shugaban kasa ya tono silar nasar Tinubu, ya caccaki Aisha Buhari

A yi hakuri, Buhari ya yi alkawarin zabe cikin lumana

A bangare guda, malamin ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa da da su yi hakuri, su kuma fito cikin dandazo don yin zabe, kada su karaya da abin da ya faru a zaben shugaban kasa na bana.

Ya ba ‘yan Najeriya da ke bukatar ganin sauyi na gari a kasar shawarin su fito su zabi wanda suke so don ciyar da kasar gaba mai daurewa.

Ya kuma yi kira da a kwantar da hankali, inda yace Buhari ya yi alkawarin tabbatar da zabe cikin aminci a kasar a bana.

A bangare guda, Daily Sun ta ruwaito yadda matasan Arewa suka yi biris da kiraye-kirayen da ake na tumbuke shugaban na INEC.

Peter Obi na jam’iyyar Labour ma ya bayyana rashin jin dadinsa ga zabo Tinubu, ya ce dan takarar na APC bai lashe zaben da aka yi bana ba.

Kara karanta wannan

Da walakin: Tinubu zai gana da zababbun 'yan majalisu da sanatoci kan wata bukata daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.