Buhari Ga Emefiele da Malami: Ku Bi Umarnin Kotun Koli Kan Tsohon Naira
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai baiwa gwamnan CBN umarnin kar ya yi biyayya ga hukuncin da Kotu ta yanke ba
- A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce tun da Buhari ya hau kan mulki bai taba hana wani bin umarnin Kotu ba
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake sukar shugaban kasan kan kin tsawaita wa'adin N500 da N1000 duk da hukuncin Kotu
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce babban bankin Najeriya (CBN) ba ya bukatar umarninsa kafin ya yi biyayya ga hukuncin da Kotun koli ta yanke kan tsoffin kuɗi.
Buhari ya karya shirunsa ne ranar Litinin game da hukuncin da Kotun koli ta yanke, wanda ya tsawaita wa'adin amfani da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa 31 ga watan Disamba.
Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce babu inda shugaba Muhammadu Buhari ya faɗa wa Antoni Janar, Abubakar Malami, da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, su ƙi bin umarnin da Kotun koli ta bayar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya kuma yi fatali da kalaman wasu cewa ba shi da tausayi, inda ya ce, "Ba'a taba yin wata gwamnati a tarihin Najeriya da ta tallafawa talaka da marasa karfi kamar gwamnati mai ci ba."
Shehu ya ƙara da cewa Buhari bai yi wani abu, "Da sanayya ko a aikace ba wanda za'a ce ya yi katsalandan ga bangaren shari'a," biyo bayan taƙaddamar da ake kan halascin amfani da tsohon kuɗi.
Garba Shehu ya ce:
"Fadar shugaban kasa ta maida martani game da damuwar 'yan Najeriya cewa har kawo yanzu Buhari bai ce uffan ba game da hukuncin Kolin koli da ya shafi batun amfani tsohon N500 da N1000 ba."
"A zahiri ba bu inda shugaban kasa ya umarci Antoni Janar da gwamnan CBN su ƙi bin umarnin Kotun da ya shafi gwamnati ko wasu tsaruka, tun da ya hau mulki a 2015, bai taɓa hana wani bin umarnin Kotu ba."
"Saboda haka bai kamata a ɗora zargi kan shugaban kasa, ana sukarsa kan ruɗanin karancin naira ba duk da hukuncin Kotu. Babu dalilin da CBN zai fake da jiran umarnin shugaban kasa ya ƙi bin umarnin Kotu."
Gwamna Abiodun Ya Tattauna da Emefiele
A wani labarin kuma Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira
Gwamna jihar Ogun ya ce nan gaba kaɗan yan Najeriya zasu barke da shewa kan sabon tsarin CBN na sauya fasalin naira.
Asali: Legit.ng