Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 5 Da Ke Hako Gawarwaki A Makabarta Suna Sayar Da Sassan Jikinsu A Ogun

Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 5 Da Ke Hako Gawarwaki A Makabarta Suna Sayar Da Sassan Jikinsu A Ogun

  • Yan sanda sun kama wasu mutane biyar kan safarar sassan jikin bil adama a garin Ijebu a jihar Ogun
  • Rundunar yan sandan ta ce mutane biyar din da aka kama a Ijebu sun amsa cewa suna sayar da sassan jiki ga masu asiri
  • Frank Mba, kwamishinan yan sanda ya tabbatar da lamarin yana mai cewa an tura binciken sashin binciken manyan laifuka

Jihar Ogun - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta kama wasu masu asiri da ke mummunan sana'arsu a Ijebu ta jihar Ogun.

Wadanda ake zargin sune: Oshole Fayemi, dan shekara 60; Osemi Adesanya dan shekara 39; Ismaila Seidu, dan shekara 30; Oseni Oluwasegun, dan shekara 69 da Lawal Olaiya, dan shekara 50.

Wadanda ake zargi
Wadanda ake zargi da hako gawarwaki daga makabarta a Ogun. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

Yan sandan hedkwatar na Odogbolu ne suka kama su ne a ranar Asabar 11 ga watan Maris na 2023, The Nation ta rahoto.

Tawagar mutanen biyar - wadanda ake zargin cewa sune suka hako gawarwaki a Ososa - yankin Ijebu kuma suka cire sassan jikinsu domin yin asiri, an kama su yayin da suke shirin sake zuwa hako wasu gawarwakin a garin.

An gano cewa DPO na Odogbolu, CSP Godwin Idehai, ya samu bayanan sirri, hakan yasa ya tattara mutanensa suka kai farmaki mabuyar wadanda ake zargin kuma aka kama su.

Kakakin yan sanda ya tabbatar da kama mutanen da ake zargi

Mai magana da yawun yan sanda, Abimbola Oyeyemi, Sufritandan yan sanda, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu cikin jawabin da suka yi na cewa suna hako gawarwaki ne suka sayarwa wadanda suke asiri.

Kwamishinan yan sanda, Frank Mba, ya bada umurcin a mika binciken sashin manyan laifuka na rundunar don zurfafa bincike.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tarwatsa Sansanin Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Samu Babbar Nasara A Jihar Arewa

Yan sanda sun kama wata babban mota dauke da bindigu a kofar shiga babban kotun jihar Osun

A wani rahoto, kun ji cewa yan sanda sun kama wata mota dauke da bindigu tana hanyar shiga harabar babban kotun jihar Osun.

Lamarin ya faru ne a lokacin da aka dawo cigaba da zaman shari'a a kotun kan korafe-korafen zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 16 ga watan Yuli kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.

Kafin zaman kotun, an ajiye yan sanda da sauran jami'an tsaro a harabar kotun da ke bincike duk wata mota da ke shiga ko fita kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164