Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Jihar Ebonyi

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Jihar Ebonyi

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun hakala Kansilan gunduma ta biyu, ƙaramar hukumar Ohaozara, jihar Ebonyi
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar lokacin da Kansila zai koma gida daga shagonsa
  • An ce matasan yankin sun fusata sun barke da zanga-zanga kan abinda ya faru da shugabansu

Ebonyi - Miyagun 'yan bindigan da ba'a sani ba sun halaka Kansila mai wakiltar gunduma ta 2 a yankin Okposi, karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi, Mista Ogbonnaya Ugwu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Kansilan, wanda ya fi shahara da SPACO ya rasa rayuwarsa hannun maharan ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar.

Harin yan bindiga.
Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Jihar Ebonyi Hoto: thenationonline
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne yayin da Spaco ke hanyar komawa gida daga shagonsa na sayar da kayan sha, wanda aka fi sani da Angle 90 a Okposi

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

Wasu majiyoyi daga garin Okpesi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun tare Mista Agwu a kusa da mahaɗar hanyar Kotun yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An tare Honorabul Kansila ne lokacin da yake hanyar dawowa daga shagonsa, wani sanannen dandalin mashaya a Okpesi, wanda ya fi shahara da Angle 90."
"Da farko sun harbe shi da bindiga ya faɗa cikin kwata, daga nan suka banka masa wuta, suka gudu suka bar wurin."

"A halin yanzun da nake magana da ku matasan N’echara da ke garin Okpesi sun fusata, sun fara zanga-zanga kan abin da ya faru," Inji wata majiya daga yankin.

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton ba'a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ba.

An Gano Gawar Mutane 10 Bayan Harin Yan Bindiga a Kaduna

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tarwatsa Sansanin Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Samu Babbar Nasara A Jihar Arewa

A wani gefen kuma, bayan harin da yan bindiga suka kai yankin karamar hukumar Zangon Kataf a Kaduna, an gano gawarwaki da yawa.

Mazauna yankin sun gano gawarwaki 10 kuma akwai tsammanin kara tsinto wasu a kauyen Unguwan Wakil biyo bayan abinda ya faru ranar Asabar.

Wata majiya ta ce rikicin ya fara ne daga gardama tsakanin wani ɗan sanda da Bafullatani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262