Karancin Naira: Dan Jarida Ya Fadi Ya Mutu Yayin Takawa Zuwa Ofis A Kasa A Ibadan

Karancin Naira: Dan Jarida Ya Fadi Ya Mutu Yayin Takawa Zuwa Ofis A Kasa A Ibadan

  • Wani dan jarida a garin Ibadan da aka fi sani da Baba Bintin ya riga mu gidan gaskiya
  • Baba Bintin ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi kasa a hanyarsa na takawa zuwa wurin aiki a ranar Asabar
  • Rahotanni sun bayyana cewa rashin tsabar kudi a hannunsa da zai shiga motar haya ta saka shi taka wa a kasa zuwa ofis

Ibadan, Oyo - Wani mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo a Ibadan da aka fi sani da Baba Bintin ya yanke jiki ya fadi ya mutu a hanyarsa na zuwa ofis a safiyar ranar Asabar.

Daily Trust ta rahoto cewa mai gabatar da shirye-shiryen ya mutu a hanyarsa na zuwa Fresh FM inda za su gabatar da shiri da Komolafe Olaiya da Olalomi a Ayefele Music House, Challenge, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Baba Bintin
Dan jarida ya riga mu gidan gaskiya yayin da ya ke takawa zuwa ofis a Ibadan. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Marigayin mai gabatar da shirye-shiryen ya saba bada bayanai kan ranar kasuwanni a jihar da kewaye.

Rahotanni sun ce yana takawa a kasa ne daga Amuloko inda ya ke zaune zuwa unguwar Challenge sakamakon rashin tsabar kudi da zai yi amfani da shi ya shiga mota ko babur zuwa ofis.

Olalomi Amole da Komolafe Olaiya sun datse shirinsu na Oyin Adun a ranar Asabar misalin mintuna ashirin yayin da suka samu labarin an garzaya da Baba Bintin zuwa asibiti.

Karancin naira da tsarin sauya kudi da babban bankin kasa, CBN, ya yi ya janyo hayaniya a kasa baki daya.

CBN din ta sauya N200, N500 da N1,000 ta haramta amfani da tsaffin amma wasu gwamnoni sun tafi kotun koli sun kallubalanci umurnin babban bankin.

Bayan hukuncin da kotu ta yanke kan tsaffin kudin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a cigaba da amfani da tsohon N200 ne kawai.

Kara karanta wannan

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

Amma daga bisani kotun ta sake halasta amfani da N500 da N1000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Amma kawo yanzu gwamnatin tarayya ba ta riga ta bi umurnin ba. Duk da cewa wasu bankuna sun fara biyan tsaffin kudin, amma ba su karba daga kwastomominsu.

Sauya Naira: Yadda ma'aikacin jami'a ya rasu a layin banki yayin neman kudin cefane

A wani labarin mai kama da wannan kun ji cewa wani bawan Allah mai suna Johnson A. Adesola da ke aiki a jami'ar LASU ya rasu a yayin kokarin cire kudi a banki.

Adesola wanda aka ce yana aiki ne a sashin kula da kudi na jami'ar ya fita daga ofis ne zuwa banki don nemo kudin da zai yi amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164