Yaro Ya Bindige Abokiyar Wasarsa Yar Shekara 3 Har Lahira A Ogun

Yaro Ya Bindige Abokiyar Wasarsa Yar Shekara 3 Har Lahira A Ogun

  • Wani yaro dan shekara 13 ya bindige wata yarinya yar shekara uku har lahira yayin da suke wasa a Jihar Ogun
  • Rundunar yan sandan jihar Ogun ta bakin kakakinta Abimbola Oyeyemi ta tabbatar da afkuwar lamarin
  • Oyeyemi ta ce tuni dai an kama wanda ake zargin, Semiu Adegesin, dan shekara 45 kan zarginsa da sakacin barin bindigarsa inda yara ke wasa

Jihar Ogun - Yan sandan jihar Ogun sun kama wani dan shekara 45 mai suna Semiu Adegesin, kan mutuwar wata yarinya yar shekara uku, Esther Samuel.

An kama Adegesin ne kan abin da aka kira sakaci da ya yi sanadin mutuwar yarinyar, The Punch ta rahoto.

Wanda ake zargi a Ogun
Mutumin da ake zargi da sakacin barin bindigarsa a inda yara ke wasa a Ogun. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin, wanda ya mallaki bindigan mafarauta, ya bar bindigan ne da harsashi ciki a fili a bayan gidansa, inda yara ke wasa.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Allah Ya Yiwa Shahrarren Dan Kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, Rasuwa

Wani dan shekara 13, Babalola, ya dauki bindigan ya juya ya fuskanci yarinyar sannan ya yi harbi.

Yan sanda sun yi martani

Mai magana da yawun yan sanda, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani Imsayi ya kai korafi hedkwatar yan sanda.

Rahoton ya ce Babalola ya harbe marigayiyar da bindigan farauta na gargajiya a kauyen Kukudi a cewar Imasayi.

Oyeyemi ya ce:

"Bayan isa wurin da abin ya faru, an tsinci wacce abin da ya faru da ita kwance cikin jininta.
"Binciken farko ya nuna cewa Semiu Adegesin, mai bindigan mafarautar, ya loda harsashi ya kuma ajiye bindigan a fili a bayan gidansa inda yara suka saba wasa.
"Daga nan ne wani dan shekara 13 Babalola ya dauki bindigan, ya kalli marigayiyar, ya harbe ta.
"An kai marigayiyar babban asibitin, Ilaro, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar ta rasu.
"Nan take aka kama mai bindigan aka tafi da shi caji ofis don amsa tambayoyi."

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

Kwamishinan yan sanda, Frank Mba, ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici kuma ya mika ta'aziyya ga iyalan mamaciyar.

Mba ya kuma yi kira ga mutane su kwantar da hankula, yana mai cewa za a yi binciken da ya dace.

Wani mutum ya sheke abokinsa ya birne gawarsa shi rikici kan kudi

A wani rahoton, jami'an tsaro sun kama wani mutum dan shekara 63 mazaunin Abuja, Taiwo Ojo, kan zarginsa da kashe abokinsa, Philip Kura.

Rahotanni sun bayyana cewa Ojo ya buga wa Philip shebur ne a kansa yayinda suke cacan baki kan wani kudi sannan ya janye gawar sa ya boye a cikin wani karamin daji, daga bisani ya birne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164