Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

  • Bata gari da ake zargin yan fashin daji ne sun kai mummunan hari a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Lere na jihar Kaduna
  • A yayin harin da miyagun suka kai a ranar Juma'a, sun kashe wani fasto sannan sun sace matarsa da wasu mutane a garin
  • Peter Mukaddas, mataimakin kungiyar Kahugu National Development Association ya tabbatar da afkuwar harin yana mai cewa suna zaman makoki

Jihar Kaduna - Wasu mahara da ake kyautata zaton yan fashin daji ne sun kashe dan wani fasto a kauye sannan sun sace matarsa a jihar Kaduna, rahoton jaridar Vanguard.

An fada wa yan jarida a wayar tarho cewa yan fashin dajin sun kai hari garuruwan Karimbu-Kahugu a karamar hukumar Lere na jihar Kaduna a safiyar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Taswirar Kaduna
Yan ta'adda sun halaka dan fasto a Kaduna, sun sace matarsa. Hoto: Vanguard Nigeria
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"An kashe yaron wani faston Baptist. Sun kuma yi awon gaba da matarsa da wasu mutane uku."

An yi kokari domin ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kaduna amma ba a yi nasara ba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Amma mataimakin kungiyar cigaban yankin mai suna Kahugu National Development Association, Mr Peter Mukaddas, ya ce suna zaman makokin wadanda suka rasu.

A cewarsa, yan bindigan sun tafi kai tsaye gidan faston lokacin da suka kai hari garin kuma suka aikata mummunan abin da suka yi.

A cikin kwanakin baya-baya nan, yan bindiga sun kai hare-hare ga malaman addini musamman fastoci a jihar Kaduna, Neja da wasu jihohin na yankin arewa.

Yan bindiga sun afka wa al'umma a masallacin Juma'a a Neja, sun halaka mutum biyu sun sace wasu da dama

Kara karanta wannan

Rudani: DSS ta Gargadi 'Yan Najeriya, Ta Ce Akwai Munanan Abubuwan Da Za Su Faru Bayan Zaben Gwamnoni

A wani rahoton kun ji cewa yan bindiga sun halaka mutane biyu sun kuma sace wasu da dama yayin harin da suka kai a jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka sace din suna cikin wata babbar mota ne da ke dawo da su daga cin kasuwar ranar Juma'a a karamar hukumar Rafi na jihar Neja.

Alhaji Ahmad Ibrahim Matane, sakataren gwamnatin jihar Neja ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya ce ba a tantance adadin mutanen da yan bindigan suka sace ba a kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164