Barayin Doya Sun Halaka Wani Ƙaramin Yaro a Gonar Mahaifin Sa
- Idan ajali yayi kira to ko babu ciwo tafiya ake, wani ƙaramin yaro ya gamu da ajalin sa a gonar mahaifin sa
- Wasu ɓarayin doya ne dai suka halaka yaron bayan ya gansu suna tafka sata a gonar mahaifin sa
- Yaron yayi ƙoƙarin kama ɗaya daga cikin ɓarayin ne lokacin da wani daban ya lallaɓo ya aika da shi barzahu
Jihar Kogi- Wasu ɓata gari sun halaka wani yaro har lahira a wata gona a ƙauyen Ikefi cikin ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu ta jihar Kogi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba, lokacin da yaron ya sanar da mahaifin sa cewa ya hango wani yana ƙoƙarin kwashe musu doya a gona.
Wani mazaunin ƙauyen, Ajibili Achonu, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan yaron sun isa gonar tare da mahaifin sa.
“Yaron ya rabu da mahaifin sa suna isa gonar, yana cikin zagayawa a gonar kawai ya ci karo da wani ɓarawo yana kwashe musu doya." Inji shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yana hango ɓarawon kawai sai ya hanzarta sanar da mahaifin sa wanda yake can a wani ɓangare na gonar"
"Yayi ta kan ɓarawon yana ihun ɓarawo, ɓarawo, bai sani ba ashe akwai wani ya laɓe a saman bishiya yana kallon abinda ke faruwa.
“Sai kawai ɗayan ɓarawon ya diro daga saman bishiyar, ya sanya adda ya halaka shi.”
Mahaifin yaron yayi saurin garzayawa gida domin sanar da mutane halin da ake ciki, nan da nan suka yo gangami domin tunkarar ɓarayin waɗanda tuni har sun ranta a na kare.
A yayin da ake cigaba da zaman jimami a ƙauyen, an kai gawar yaron ɗakin ajiye gawarwaki a Ajaka, hedikwatar ƙaramar hukumar. Rahoton Tori.ng
Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP William Aya, yayi alƙawarin tuntuɓar DPO ɗin yankin domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un: Allah Ya Yiwa Basaraken Abuja, Etsu Na Yaba Rasuwa
A wani labarin na daban kuma, wani babban basaraken Abuja, ya rigamu cikawa gidan gaskiya.
Basaraken ya rasu ne akan hanyar sa ta zuwa masallaci.
Asali: Legit.ng