Wata Mata Ta Kai Karar Mijinta Kotu Saboda Tauye Hakkinta Na Aure

Wata Mata Ta Kai Karar Mijinta Kotu Saboda Tauye Hakkinta Na Aure

  • Wata mata ta bayyana gajiya da zama da mijinta, inda tace sam ba ya ba ta abin da take bukata na hakkin aure ko kadan
  • Hakazalika, ta zarge shi da rashin kulawa da ita da ‘ya’yanta, inda ta bukaci a balle igiyar auren da ke tsakaninsu gaba daya
  • Ana yawan samun lamuran da suka shafi zamantakewar aure da ke kaiwa ga zaman kotu a Najeriya, musamman a irin wannan yanayin

Nyanya, Abuja - Wata mata ‘yar kasuwa, Mrs Joy Abu ta maka mijinta Daniel a kotun kostomare da ke Nyanya a Abuja a ranar Alhamis bisa zargin yana tauye mata hakkin kwanciyar aure.

Joy, wacce ke zaune a yankin Jikwoyi a Abuja ta kuma ce, mijinta bai da halin kula da iyali, don haka nema ta zo gaban alkali.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: A rikicin shiga banki, mata ta gasawa dan sanda cizo, ya maka ta a kotu

Matar, da ta nemi a balle igiyar aurenta da Daniel ta ce, mijin nata ba ya kula da ita da ‘ya’yanta ko kadan, Daily Trust ta ruwaito.

Mata ta kai mijinta kotu saboda rashin samun jima'i
Yadda kotu ya zauna kan batun aure | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Mijina na da halin ko-in-kula, cewar matar aure Joy

A cewarta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A zahirance mijina na hana hakkina na aure; bai damu da sanin meye nake ji ba, bai san cewa aure ba lamari ne na abinci kadai ba.
“Miji mai kula da iyali zai lura da bukatun kawa-zucin matarsa.”

Da take bayyana abin da take bukata daga mai shari’a, ta ce tana son a raba aureus tare da umartar mijin nata Daniel yale ya ba ta N100,000 duk wata don kula da ‘ya’yansu.

Daniel ya musanta zargin da ake masa

Daniel dai ya tubure a gaban kotu, inda ya kekasa kasa yace sam ba gaskiya bane, shi dai yana kula da ‘ya’yansa da kuma matar tasa Joy, rahoton kafar labarai ta Tori.

Kara karanta wannan

"Na Shiga Uku": Wani Dan Najeriya Ya Koka Bayan Gayyatar Wata Budurwa Ta Kwana A Gidansa, Ya Wallafa Bidiyo

Mai shari’a Labaran Gusau na kotun ya saurari dukkan bangarori, inda ya dage ci gaba da sauraran batun zuwa ranar 30 ga watan Maris na wannan shekarar.

Ba sabon abu bane a Najeriya mace ta maka mijinta a kotu domin bukatar karan kanta, musamman lamarin da ke da alaka da lafiya da zamantakewar aure.

A wani labarin kuma, mijin ne ya nemi a raba auren saboda matarsa da 'ya'yansa na haduwa su lakada masa dukan kawo wuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.