“Da Kishiyar Gida Ko Ta Waje?”: Matar Aure Ta Zabi Wacce Ta Fi So a Bidiyo

“Da Kishiyar Gida Ko Ta Waje?”: Matar Aure Ta Zabi Wacce Ta Fi So a Bidiyo

  • Wata matashiyar mata ta bayar da amsa cikin hikima yayin da aka mata tambaya da ya shafi aure
  • Matar auren na ta murmusawa yayin da take bayyana dalilanta na zabar kishiyar gida sama da kishiyar waje
  • Koda dai matar ta ce bata jin dadi idan ta tuna batun kishiya, ta fi dacewa sama da ta waje

A cikin wani bidiyo da @al-ameen ya wallafa a TikTok, wani mai tambayoyi ya tsayar da wata mata mai suna Faridah don yi mata yan tambayoyi.

Mai tambayan ya fara da neman sanin ko tana da aure sai ta ce eh, sannan sai ya ci gaba da tambayarta ko za ta fi so ace mijinta ya tara yan mata da yawa a waje bisa ga yi mata shiya.

Matar aure tana amsa tambayar wani matashi
“Da Kishiyar Gida Ko Ta Waje?”: Matar Aure Ta Zabi Wacce Ta Fi So a Bidiyo Hoto: @al-ameen
Asali: UGC

Matashiyar ta fara dariya kafin ta amsa masa. Ta ce tambaya ce sarkakiya amma sai ta ci gaba da cewa babu matar da ke son batun kishiya duk da cewar addininta ta Islama ta yarda da haka.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wata Mata Mai Shayarwa Ta Faɗi Yadda Ta Dauki Cikin Wata 5 Bata Sani Ba, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Matar ta fi son kishiyar gida

Matar wacce ta kasance musulma ta ce idan har sai ta zabi daya a cikin abubuwan guda biyu, toh za ta zabi wanda ya yi daidai da addininta wanda shine kishiyar gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai tambayar ya yi mata godiya a kan lokacinta da ta ara masa, yana mai cewa dan takaitaccen hiran ya zo karshe.

Masu amfani da TikTok da suka yi martani ga bidiyon, sun ce matar ta bayar da amsa cikin hikima.

Jama'a sun yi martani

@fadhilaAjefunija ta yi martani:

"Kalli matar, tana dauke da kwanciyar hanka;li, tana da kyau kuma."

@imageoflife ta ce:

"Mace mai tsananin wayo. Bata so ta jefa rayuwarta a hatsari ta hanyar yan matan mijinta."

@yusuf_shade ta kuma yi martani:

"Wow"Wow…Ina kaunarta."

@Ayinla_bisola:

"Zai kuma kasance da yan mata a waje duk da mata hudu...ba maza bane."

Kara karanta wannan

Ali Ya Ga Ali: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a “Go Slow” Tana Gaggawa Ta Koma Gida Don Ta Yi Dare a Waje

@everything_jums:

"Amsa mafi dacewa kafin ya je ya kwaso cututtukan STD da HIV."

Kalli bidiyon a kasa:

Mai gidan haya ya fatattaki dan haya bayan ya kashe miliyoyi wajen gyara gida

A wani labari na daban, wani matashi ya koka sakamakon tashinsa da wani mai gidan haya ya yi bayan ya kashe miliyoyin kudi wajen gyara gidan ya zama yadda yake so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel