An Sace Min Wayoyi Na a birnin Tarayya Abuja, Sanatan APC Ya Koka
- Wasu masu halin ɓera sun yi awon gaba da wayar sanatan jam'iyyar APC a birnin tarayya Abuja
- Ɓarayin dai sun sace wayar sanata Uzor Orji Kalu a wajen karɓar satifiket ɗin lashe zaɓen sa wanda hukumar INEC ta bayar
- Sanata Uzor Kalu ya bayyana cewa tuni ya sanar da kamfanin layukan wayoyin nasa halin da ya tsinci kan sa a ciki
Abuja- Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa an sace wayoyin sa guda biyu ɗauke da layukan MTN da Glo.
Sanata Kalu ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook inda ya gargaɗi mutane da kada su yarda da duk wani saƙo da ka iya fitowa ta hannun wayoyin.
Kalu yace an lalube masa wayoyin ne a yayin da yake karɓar satifiƙet ɗin lashe zaɓen sa a ɗakin taro na ƙasa-ƙasa dake birnin tarayya Abuja. Rahoton Vanguard
Ya miƙa ƙoƙon baran sa ga al'umma kan su taimaka su bayar da muhimman bayanan da ka iya sanyawa a gano wayoyin nasa guda biyu, inda ya ƙara da cewa tuni har ya sanar da kamfanunnikan layukan halin da ake ciki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ina sanar da jama'a cewa suyi hattara da duk wani abun rashin gaskiya wanda ya fito daga waya ta da lambobin waya ta" Inji shi
“A lokacin amsar satifiket ɗin lashe zaɓe a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa dake birnin tarayya Abuja, waya ta ɗauke da layukan MTN da Glo, wasu waɗanda ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da ita."
“Tuni har na sanar da kamfanunnikan layukan halin da ake. Ina roƙon ku da kada ku ji shakkun bayar da kowane irin bayani mai muhimmanci."
Gaskiya Ta Fito Fili, INEC Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Zaɓen Tambuwal Da Sauran Ƴan Majalisun Tarayya a Sokoto
Jam'iyyar ADP Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa Kan Ɗan Takarar Gwamnanta Na Kaduna
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar ADP ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa kan ɗan takarar gwamnan ta na jihar Kaduna.
Jam'iyyar ta fito fili ta bayyana halin batun takarar sa yake ciki a jihar ta Kaduna.
Asali: Legit.ng