Sojoji Sun Kai Harin Bazata Sansanin Masu Garkuwa, Sun Ceto Kwamishina Da Aka Sace
- Jaruman sojojin Najeriya na 13 Birgade a Calabar, karkashin Operation Akapkwu sun kai wa masu garkuwa da mutane farmaki
- Dakarun sojojin sun yi nasarar kai wannan farmakin ne sakamakon bayanan sirri da suka samu game da bata garin
- A yayin harin na bazata, sojojin sun ragargaji masu garkuwan, sun kuma ceto wata kwamishina a jihar, Mrr Gertrude Njar wacce aka sace
Cross Rivers - Dakarun sojojin Najeriya na 13 Birgade, Calabar, karkashin Operation Akpakwu, sun ceto kwamishinan harkokin mata a Cross Rivers, Mrs Gertrude Njar, da aka sace ta.
Sanarwar cetonta na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kyaftin Dorcas Aluko, mai magana da yawun 13 Birgade, ta fitar ranar Laraba a Calaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sace kwamishinan ne a ranar 1 ga watan Fabrairu a Mayne Avenue a Calabar, kamar yadda Zagazola ya rahoto.
Aluko ta ce:
"Bayan samun bayanan sirri kan inda aka ajiye wacce aka sace, dakarun sojojin sun dana wa masu garkuwar tarko kusa da Peter Effiong Creek, Messembe, Jebs.
"Jaruman sojojin suka fito suka afka wa masu garkuwar ba zato ba tsammani yayin da suke neman wacce aka sace.
"Sakamakon hakan, bata garin sun tsere sun bar wacce aka sace din."
Ta kara da cewa dakarun sojojin sun bi sahun bata garin da suka tsere suka shiga daji.
A cewar Akuko, wacce aka ceto tana nan a asibiti tana samun kulawa, daga bisani za a sako ta.
Ta kara da cewa:
"Kwamandan Birgade na 13 ya yaba wa dakarun sojojin bisa jajircewarsu ya kuma bukaci su cigaba da yin kokarin kawar da dukkan bata gari a yankin.
"Ya kuma yi kira ga al'umma su cigaba da ba wa jami'an tsaro bayanai masu amfani kuma a kan lokaci a unguwanninsu."
DSS sun kama wasu jiga-jigan PDP uku a Kaduna kan zargin 'shirin tada zaune tsaye' yayin zabe da ke tafe
Yan sandan farin kaya na DSS sun kama mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Kaduna na jam'iyyar PDP, Sa'idu Adamu.
An kama shi tare a El-Abbas Mohammed da Talib Mohammed shugabannin matasa na PDP kan zargin shirin tada tarzoma yayin zaben gwamna da yan majalisu.
Asali: Legit.ng