"Mu ƴan APC ne, Amma PDP Zamu Zazzagawa Kuri'un Mu a Zaɓen Gwabna"

"Mu ƴan APC ne, Amma PDP Zamu Zazzagawa Kuri'un Mu a Zaɓen Gwabna"

  • Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci ƴan ƙasa dasu zaɓi duk ɗan takarar da yayi musu daga kowacce jam'iyya
  • Jigo a jam'iyyar APC ɗin yace saboda haka zasu zaɓi jam'iyyar PDP saboda APC dake mulkin jihar da cewa ta ɓarar fatan da mutane sukai mata
  • Jigon APCn yace lokaci yayi da za'a dinga bawa matasa dama a jihar, ta hanyar zaɓar ɗan takarar na jam'iyyar PDP

Zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisu dai yazo yabar baya da ƙura, yayin da muke tunkarar zaɓen Gwabnoni.

Wasu sun amshi sakamakon su a hannun hagu, wasu kuma nasu sakamakon a hannun dama suka amshi nasu.

Amma a wani yanayi na maida agogon APC baya a jihar Nasarawa, wani jigo a jam'iyyar APC, Obiya Yahaya-Doma yayi wani gagarumin kira ga mutanen sa akan suyiwa ɗan takarar jam'iyyar PDP rubdugun ƙuriu, watau David Ombugadu.

Kara karanta wannan

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

AA Sule
Mu ƴan APC ne, Amma PDP Zamu Zazzagawa Kuri'un Mu a Zaɓen Gwabna Hoto: UGC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jigon jam'iyyar APC ɗin, yayi wannan kiran ne a wani hira da manema labarai sukayi yi jiya a lafiya, babban birnin Nasarawa.

Jigon yace, kiran ya zama abu mai muhimmanci duba da nagartar ɗan takarar na jam'iyyar PDP da kuma tsarin da yazo dashi da yake so ya cimma idan yaci zaɓe.

Yace Ombugadu nada tarihi a rayuwar sa ta siyasa wajen kyautatawa mutane a zuwan sa majalisar tarayya dake wakiltar Akwanga/Nassarawa-Eggon/Wamba daga 2011-2019.

Ya ƙara tabbatarwa manema labarai cewar, yayi da Ombugadu yake a majalisa, ya samar wa matasa aiki, ya kawo ayyukan raya ƙasa gamida asibitoci, makarantu da kuma wutar lantarki.

A kalaman sa:

"Ya kuma samar da tuka-tuka a duk wata mazaɓa. Har aiki yayi a wajen mazaɓarsa. Idan mutum zaiyi wannan aikin a matsayin mai wakilci, inda ace gwamna ne mai zai faru".

Kara karanta wannan

Bayan Ya Garzaya Kotu, Peter Obi Ya Aikewa Magoya Bayansa Da Wani Muhimmin Gargaɗi

Yahaya-Doma yayi nuni da cewa, lokaci yayi da za'a dinga bawa matasa dama a jihar, ta hanyar zaɓar ɗan takarar na jam'iyyar PDP dake cikin shekarun sa na 40.

Koda aka tambaye shi ko an sahale musu suna APC su zaɓi ɗan PDP, Yahaya-Doma yace ko Muhammadu Buhari yace yan Najeriya suje su zaɓi duk wanda suke so a kowacce jam'iyya ta hanyar duba nagartar ɗan takara.

Sai yaci gaba da cewa:

"Mu yan APC ne, amma ɗan takarar jam'iyyar PDP zamu zaɓa a zaɓen gwamna mai zuwa duba da nagartar sa da ayyukan alherin da yayi.
"Wannan shine salon da ake yayi a zaɓen 2023. Yawancin yan jam'iyyar APC a ko ina na jihar nan, sun yanke shawarar zaɓen ƴan takarkaru masu tarihin bautawa jama'a batare da la'akari da addini ko siyasa ba".
"Banyi wani abu mara kyau ba saboda Muhammadu Buhari shugaban jam'iyyar mu yace mu zaɓi kowani ɗan takara da muke so a ko ina yake" Inji shi

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Jihar Kano: Shin Tarihi Na Shirin Sake Maimaita Kansa Ne

Ya kuma zargi gwamnatin dake mulkin jihar da cewa, batayi abinda mutane suka zaɓe ta tayi musu ba, kuma ta barar da kyakkyawan fatan da sukai mata.

Daga karshe sai yayi kira ga ɗaukacin mutanen Nasarawa dasu guji siyasa akan addini ko kabilanci. Ya bukaci mutanen jihar da su sanya fatan ganin jihar taci gaba akan komai, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Yadda Tsohon Hafsun Sojoji Ya Sace N2bn a Asusun Sojan Sama – Shaidan EFCC a Kotu

Lauyoyin hukumar EFCC sun kira Okechukwu Akube a matsayin shaida a shari’arsu Adesola Amosu Tsakanin 2014 da 2015.

Air Marshall Adesola Amosu shi ne Shugaban hafsun sojojin sama a Najeriya EFCC ta ce Hafsun da wasu tsofaffin jami’ai sun hada-kai sun sace N2bn daga asusun gidan sojoji a 2014

Punch ta ce Okechukwu Akube ya yi wa Alkali bayanin yadda wadanda ake zargi suka karkatar a Naira Biliyan biyu daga asusun kar-ta-kwana na sojin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida