“An Kama Ka Hannu Dumu-Dumu’: Bidiyon Yadda Yaro Ya Barnata Milo, Barci Ya Dauke Shi Ya Jawo Cece-Kuce

“An Kama Ka Hannu Dumu-Dumu’: Bidiyon Yadda Yaro Ya Barnata Milo, Barci Ya Dauke Shi Ya Jawo Cece-Kuce

  • An yada wani bidiyo mai ban dariya na yadda barci ya dauke wani yaro karami daidai lokacin da ya bude gwangwanin Milo yana sha
  • An ga bakin yaron a wangale, alamun da ke nuna ya manta ma da hukuncin da ake yiwa yara idan suka aikata barna irin wannan
  • Jama’a a kafar TikTok sun yi nishadi, da yawa sun yi martani da cewa, tabbas an kama shi hannu dumu-dumu kenan yana laifi

A bidiyon da aka yada a TikTok, an ga wani yaro da barci ya kwashe shi a lokacin da ya tasa gwangwanin Milo a gaba yana sha.

Bidiyon ya nuna yadda yaron ya cika hannunsa da Milo, ga dai alamun ya jagwalgwala kayan shayin a jikinsa.

A lokacin da yake barcinsa, an ga kansa ya tankware gefe bayan ya sha ya koshi da Milo da watakila aka ajiye ya dauko ya barnata.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Yadda aka kama yaro na tsaka da barnata Milo
Hotunan yadda yaro ya barnata Milo | Hoto: @pu's'sypanda77
Asali: TikTok

An kama shi hannu dumu-dumu

Wani mutum ya zo dakiku kadan bayan da yaron ya gama barnarsa don duba meye ya faru kafin daga bisani ya dauke gwangwanin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya nuna daya hannun yaron cike da Milo yayin da daya kuwa ke cikin gwangwanin, an kama shi dumu-dumu.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutum 3000 ne suka yi martani kan bidiyon, yayin da sama da mutum 68,000 suka yi dangwalen nuna sha’awa.

Ga abin da jama’a ke cewa:

D Loml:

"Mai shari’a, wanda nake karewa sharri aka yi masa. Ba zai iya shanye fakitin Milo ba ma...duk wannan kitsawa aka yi mai shari’a.”

Your baby:

"Barkewa da barci a tsakiyan aikata laifi.”

Eloho Faith525:

"Sai na tuna yadda na shanyewa mahaifina Don Simon dinsa, kawai barci ya dauke ni ina tsaka da laifi haka ya jira sai da na tashi.”

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutum 6 Sun Mutu, An Sace Wasu 50 Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Wata Jihar Arewa

Bag_Of_Cheese01:

"Irin haka ake kama wasu mazan hannu dumu-dumu amma a haka za su musanta.”

Yomi Oladipupo:

"Ko Falana ne ba zai kare ka da wannan laifin ba.”

A wani labarin kuma, an ga yadda wani mutum ya ga kifi a bakin teku, amma ya mai dashi cikin ruwa a madadin tafiya dashi don cinyewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.