Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan bindiga, Sun Ceto Kwamishina a Kuros Riba
- Sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da kwamishinar harkokin mata ta jihar Kuros Ribas daga hannun masu garkuwa
- A wata sanarwa da rundunar Biged 13 da ke Kalaba ta fitar, ta ce bayan samun bayanai, Dakaru suka kai samame mafakar
- A halin yanzu kwamishinar na karɓan magani a hannun Sojoji kafin daga bisani su sallameta ta koma cikin iyalai
Cross River - Sojojin rundunar Birged ta 13 da ke Kalabar, sun ceto kwamishinar harkokin mata ta jihar Kuros Riba, Misis Gertrude Njar, daga sansanin masu garkuwa da mutane.
Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da Kaftin Dorcas Aluko, jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar Birged 13 da ke Kalaba ta fitar ranar Laraba, kamar yadda Punch ta rahoto.
A ranar 1 ga watan Fabrairu, 2023, mahara suka yi awon gaba da kwamishinar matan a yankin Mayne Avenue da ke Kalaba ta kudu.
Aluko ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yayin ɗaukar mataki kan bayanan sirrin da muka samu na inda kwamishinar take tsare, dakarun soji sun kai samamen kwantan bauna kan masu garkuwa a yankin Peter Effiong Creek."
"Cikin dabaru da jajircewa, sojojin suka mamayi masu garkuwan a ƙoƙarinsu na gano inda matar take, ana musayar wuta 'yan bindigan suka tsere suka bar kwamishinar a nan."
Kaftin Aluko ta ƙara da cewa a halin yanzun gwarazan Sojojin sun bazama neman 'yan ta'addan, waɗanda suka ari na kare yayin musayar wuta.
Ta ƙara da cewa tuni suka kai kwamishinan Asibiti domin duba lafiyarta daga bisani zasu sallameta ta koma gida.
PM News ta rahoto Kaftin Aluko na cewa:
"Kwamandan Birged 13 ya yaba wa Sojojin bisa jajircewarsu kana ya roki su ci gaba da haka kan dukkan 'yan ta'addan da suke yankin da ke karkashin kulawar rundunar."
"Muna kira ga mutane da su ci gaba da baiwa dakarun haɗin kai da ba su sahihan bayanai game da ayyukan yan ta'adda a yankunansu."
Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Bijilanti da Dama a Jihar Kaduna
A wani labarin kuma Yan bindiga sun halaka yan banga 6 a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
Wani mamban ƙungiyar 'yan bangan watau Yan Bijilanti, ya ce suna cikin jimamin rasa yan uwansu lokaci guda da yammacin Laraba.
Kawo yanzu babu wata sanarwa daga hukumar yan sanda ko gwamnatin Kaduna game da sabon harin.
Asali: Legit.ng