Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Bijilanti da Dama a Jihar Kaduna
- Mahara sun yi ajalin yan sa'kai mutum 6 a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
- Wani mamban yan Bijilanti ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni aka musu Sallar Janaza kamar yadda Musulunci ya umarta
- Har yanzun ba'a ji daga gwamnatin Kaduna ko rundunar 'yan sanda ba kan sabon harin na yau Laraba
Kaduna - Yan bindigan daji sun halaka jami'an tsaro da ake kira 'yan Bijilanti guda 6 a shingen binciken Awaro dake yammacin Birnin Gwari, ƙaramar hukuma Birnin Gwari a Kaduna.
Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya auku ne yau Laraba 8 ga watan Maris, 2023 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Wani mamban ƙungiyar 'yan Bijilanti, Usman Babangida, cikin jimamin rasa abokan aikinsa, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigan sun mamayi wurin da yawansu.
Ya ƙara ca cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi yayin da suka haɗu da Yan Bijilanti, suka yi ajalin aƙalla mutane shida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa tuni aka yi wa waɗanda suka mutu Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Babangida ya bayyana cewa maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne jim kaɗan bayan sun yi artabu da wata tawagar yan bindigan a kauyen da ke kusa, Bugai.
Amma Jami'in ya ce ba zai iya tabbatar da adadin yawan yan bindigan da suka mutu ba a musayar wutan da suka yi tsakaninsu.
A kalamansa, Babangida ya ce
"Da kusan karfe 4:00 na yamma abun ya faru lokacin da 'yan fashin suka zo wucewa ta shingen Awaro, nan take suka farmaki Dakarun Bijilanti daga ganinsu."
"Sun kashe mutane Shida da suka gani a wurin, wasu mazauna ƙauye ne suka ga gawarwakinsu daga baya aka dauko su zuwa cikin gari," inji shi.
Har kawo yanzun ba bu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko hukumar 'yan sanda. Da aka kira kakakin yan sanda, Muhammad Jalige, an ji yana waya da wani.
Yan bindiga sun sace mata da 'ya'yanta biyu a Kaduna
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sake Shiga Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da mutane sama da 10
Wasu maharan sun shiga yankin karamar hukumar Kagarko, sun yi garkuwa da wata matar aure, yaranta biyu da wasu mutane 9.
Mazauna yankin sun ce mutane tara sun yi nasarar gudowa daga sansanin yan bindigan kawo yanzu.
Asali: Legit.ng