Za Mu Karbe Nasarawa Daga Hannun APC, Dan Takarar Gwamnan SDP
- Dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Nasarawa ya ce jam'iyyarsa za ta karbe mulki a jihar
- Muhammad Mustapha, dan takarar na SDP ya ce kujerun yan majalisar tarayya da jam'iyyarsa suka ci a zaben ya nuna mutane suna goyon bayan sa
- Mustapha ya kara da cewa mutanen da za su fito zaben jiha sai rubanya na tarayya saboda mutanen jiha sun san cewa gwamna da yan majalisar jiha sun fi kusa da su
Nasarawa - Muhammad Mustapha, dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Nasarawa, ya ce yana da tabbacin lashe zaben gwamnan jihar, Daily Trust ta rahoto.
Mustapha cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na Channels TV ya ce gwamnatin APC ba ta da wani abu da za ta yi wa mutanen jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Mutanen Nasarawa sun riga sun yi magana cewa za su bani wannan nasarar; ta hanyar zaben SDP. Daga zaben majalisar tarayya, ina da sanatoci biyu cikin uku da yan majalisar wakilan tarayya biyu cikin biyar. Hakan ya nuna cewa muna jiran rantsarwa ne kawai.
"Kana iya ganin cewa mutanen Nasarawa na son canji. Abin da yasa na samu yan majalisar tarayya shine mutane sun gaji da mulkin gwamnatin Nasarawa.
"Mutane za su zabi SDP saboda sun gaji da APC da PDP, suna son gwada sabuwar jam'iyya."
Da ya ke amsa tambaya kan yiwuwar nasara, Mustapha ya ce:
"Idan kana magana zaben jiha, wasu lokutan yana canjawa daga zaben majalisar tarayya.
"Ko yawan mutanen da suka fito zabe wannan karon za su ninka na baya saboda mutane sun fi fitowa zaben jiha don ya ci kusa da su da zaben majalisar kasa.
"Ina tabbatar muku munyi aikin mu. Kasancewar SDP sabuwar jam'iyya a jihar Nasarawa ya nuna cewa mutane sun yarda da jam'iyyar kuma za su kada mata kuri'a.
"Kuma ni ba bako bane a siyasa, ni dan takarar APM ne a 2019 kuma dukkan mu mun yanke shawarar komawa SDP. Hakan na nuna cewa iskar mulki ya canja. Ina tabbatar maka za mu karbe mulki a Nasarawa."
Ayo Fayose: Ina nan a jam'iyyar PDP
A bangare guda, jigon PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya karyata rahoton cewa ya fita daga jam'iyyar PDP.
Fayose ya yi karin bayani inda ya ce yana nan daram a PDP amma ya dan koma gefe guda ne don ya samu damar furta wasu maganganu a matsayinsa na dan kasa.
Asali: Legit.ng