Amurka Na Duba Yiwuwar Haramta Amfani da Manhajar TikTok Ga ’Yan Kasar

Amurka Na Duba Yiwuwar Haramta Amfani da Manhajar TikTok Ga ’Yan Kasar

  • Gwamnatin Amurka ta ce za ta tabbatar da haramta manhajar TikTok a kasar saboda wasu dalilai na tsaron kasar
  • Amurka na zargin TikTok da yiwuwar siyar da bayanan tsaro da na sirri ga gwamnatin kasar China mai gasa da ita
  • TikTok ya bayyana alakarsa da gwamnatin China da kuma yadda yake kula da bayanan jama’a, musannan na Amurka

Kasar Amurka - Kasar Amurka na shirin haramta amfani da manhajar TikTok mallakin dan kasuwan kasar China da sauran shafukan sada zumunta na kasashen ketare.

A cewar Amurka, wannan zai taimakawa kasar wajen magance barazanar tsaro da ka iya samunta saboda leken asirin da manhajojin waje ke yi.

A cewar rahoton BBC, fadar shugaban kasar Amurka ta ce tana goyon bayan wannan yunkuri na dakatar da manhajar TikTok.

Za a haramta TikTok a Amurka
Yadda Amurka ke shirin haramta TikTok | Hoto: lawfmng.com
Asali: UGC

A tun farko, an ce gamayyar jam’iyyun siyasar kasar biyu ne suka bijiro da kudurin tabbatar da an soke tare da haramta amfani da manhajojin waje a Amurka.

Kara karanta wannan

Jarumin Kannywood, Tijjani Asase, Ya Angwance Da Zukekiyar Amaryarsa, Hotuna Sun Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin da yasa Amurka za ta katse TikTok

Jake Sullivan, mataimaki na musamman kan harkokin tsaron fadar White House ya ce, wannan kuduri ne na kokarin kare gwamnatin Amurka daga fadawa tashin hankali da barazanar tsaro.

Hakazalika, kuduri ne da ya samu karbuwa da goyon bayan da yawan mambobin jam’iyyun Democrats da Republican a majalisar dattajai ta kasar.

Amurka na zargin cewa, kasar China na kokarin kutse kan harkokin tsaronta, wannan lamari na ci gaba da daukar hankali.

A cewar Amurka, gwamnatin China za ta iya tursasawa kamfanoni irinsu TikTok don ba da bayanai na sirri game da kasar ta Amurka.

TikTok ya magantu kan alakarsa da gwamnatin China

Sai dai, shugaban manhajar TikTok, Shou Chew a wannan makon ya ce, kamfanin nasa bai taba karbar wata bukata daga gwamnatin China game da bayanan sirri ba.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Aiki ya kankama, an yi mota mai amfani da ruwa a jami'ar Arewacin Najeriya

Hakazalika, ya ce kamfanin ba zai taba amincewa da bukatar ba da bayanan da ka iya zama na kutse ga China ba, CNN ta ruwaito.

A bangare guda, kamfanin na TikTok ya dauki matakin saryar da daukar bayanai masu muhimmanci na Amurkawa a kan manhajar.

Hakazalika, kamfanin na duba yiwuwar kulla yarjejeniyar sulhu da shugaba Joe Biden na Amurka don barin manhajar ta ci gaba da aiki a Amurka.

A Najeriya kuma, hukumar Hisbah a Kano na ci gaba da daukar mataki kan masu yada badala da rashin tarbiyya a TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.