Shugaban ’Yan Sanda Ya Tura Sabon CP Kano, Ya Soke Tura CP Balarabe Sule Bayan Wata Zanga-Zanga
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana shirinta na tabbatar da tsaro a lokacin zaben gwamna da ‘yan majalisun dokoki a jihar Kano
- An tura sabbin manyan jami’an da su sanya ido kan kananan hukumomin jihar bayan soke tura wani sabon kwamishina a jihar
- An samu tsaiko a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Kano a ranar 25 ga watan Faburairu
Jihar Kano - Sufeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya soke tura CP Balarabe Sule a matsayin kwamishinan jihar Kano.
A madadinsa, IGP ya tura CP Faleye Olaleye daga jihar Ebonyi don rike mukamin kwamishinan a lokacin zaben gwamnoni da za a yi, Daily Nigerian ruwaito.
Jam’iyyar NNPP a jhar Kano ta yi zanga-zanga bayan labarin cewa, za a tura CP Balarabe Sule. ACP Adamu Babayo da ACP Abubakar Shika zuwa jihar.
Zargin da ake kan manyan jami’an da aka soke turowa Kano
A cewar majiyoyi, manyan jami’an uku da aka turo Kano sun taba aiki tare kuma sun kasance masu nuna goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa, rahoton Sahelian Times.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An ruwaito cewa, IGP ya saurari koken zanga-zangar ‘yan NNPP, inda ya soke tura jami’an.
Hakazalika, IGP ya turo manyan jami’ai zuwa jihar Kano don tabbatar da tsaro a lokacin zaben Asabar mai zuwa.
Jami’an da za su yi aiki a Kano a lokacin zabe
A cewar rahoton, an tura AIG Sani Dalijam domin kula da Zone 1 jihar ta Kano, yayin da Ita Lazarus Uko-Udom da DCP Umar Iya za su kula da Kano ta tsakiya.
A bangare guda, DCP Abdulkadir El-Jamel zai sanya ido kan kananan hukumomin Gaya, Rogo, Albasu, Takai, Ajingi, Garko, Wudil da kuma Sumaila.
Kananan hukumomin Rano, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Kibiya da Tudun Wada a Kano ta Kudu kuwa za su kasance karkashin kulawar DCP Adamu Ngojin.
A Kano ta Arewa, an tura DCP Abaniwonda Olufemi da ACP Adamu Sambo don tabbatar da tsaro a lokacin zaben.
A cewar rahoton da jaridar ta samo daga ‘yan sanda, DCP Auwal Musa zai rike cibiyar CID tare da DCP Aminu Maiwada da zai kula da ayyuka a ofishin umarni na ‘yan sanda a lokacin zaben.
An samu rikici a Kano a lokacin zaben shugaban kasa, har ta kai aka kama dan majalisa, aka gurfanar dashi amma daga baya aka yi belinsa.
Asali: Legit.ng