An Kama Wani Mai Gida Bayan Ya Kai Sunayen Masu Haya Gidansa Shaharariyar Matsafa Bayan Sun Samu Saɓani

An Kama Wani Mai Gida Bayan Ya Kai Sunayen Masu Haya Gidansa Shaharariyar Matsafa Bayan Sun Samu Saɓani

  • Yan sanda sun cafke wani mai gidan haya kan zarginsa da kai sunan yan hayarsa wurin boka
  • Ana tuhumarsa da aikata laifin hadin baki da neman yin shari'a ta hanyar gwaji
  • Rahotanni sun nuna cewa boka ya kira yan hayar ya ce su kawo kansu wurinsa idan ba haka ba za su mutu

Jihar Legas - Yan sanda a Legas sun gurfanar da wani Okechukwu Chukwunahi, mai gidan haya dan shekara 44, kan kai sunayen masu haya gidansa wurin boka, rahoton The Cable.

Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta rahoto cewa an gurfanar da Chukwunahi a kotun majistare a Ojo, ranar Talata.

Gudumar Kotu
An gurfanar da mai gida a kotu kan kai sunan masu haya a gidansa wurin boka a Legas. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan sandan na tuhumarsa da hadin baki shari'a ta hanyar gwaji.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Mai shigar da kara ya fada wa kotu abin da ya faru tun farko

Simon Uche, lauyan mai shigar da kara, ya fada wa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin a watan Fabrairu a Ira Quaters.

Ya ce Chukwunahi ya kai sunayen yan gidan hayarsa zuwa gidan tsafi na "Arusi Okija" bayan sun samu rashin jituwa.

Uche ya ce bokan ya kira yan gidan hayan cewa su taho wurinsa da kansu idan ba haka ba suna iya mutuwa.

Mai shigar da karar ya ce wadanda suka shigar da karar sune Onyeka Ibeabuchi da Chimezie Ezeuka.

Ya ce da farko wanda aka yi karar ya kai korafi wurin sulhu da kotu bisa rashin jituwar da ya shiga tsakaninsa da yan hayan.

Amma ya yanke shawarar ya kai su wurin boka saboda bai gamsu da hukuncin da kotu ta yi ba.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Baya Ga Dogon Layi a Banki, Kwastomomi Sai Sun Ba Da Cin Hanci Kafin Su Iya Shiga Banki

Dan sandan mai shigar da kara ya fada wa kotu cewa laifin ya saba wa sashi na 127 da 411 na dokar masu laifi na Legas, 2015.

An bada belin wanda ake tuhuma

Da ya ke yanke hukuncin, J.K Layeni, alkalin kotun ya bada belin wanda ake zargin kan N300,000 da mutum biyu da suka karbe shi.

Ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Maris.

Wani mutum ya kashe abokinsa saboda rikici kan kudi

A wani rahoton, yan sanda sun cafke wani dan shekara 63 da ke zaune a Abuja mai suna Taiwo Ojo, kan zarginsa da kashe abokinsa mai suna Philip Kura.

Wanda ake zargin ya halaka Kura ne saboda sabani da suka samu game da kudi a cewar rahotanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164