Ma'aikaci Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Satar Kuɗin Kamfani

Ma'aikaci Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Satar Kuɗin Kamfani

  • Wani ma'aikacin wani kamfani a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu saboda cin amanar kamfanin sa
  • Ma'aikacin kamfanin dai yayi sama da faɗin da kuɗaɗen kamfanin waɗanda yawan su ya kai naira miliyan goma
  • Ma'aikacin kamfanin ya shafawa idon sa toka yace sam bai aikata wannan laifin na sata da ake tuhumar sa da shi ba

Legas- An gurfanar da wani mutum mai suna Folarin Ajayi, a gaban wata kotun majistare mai zaman ta a Ogba, cikin Ikeja, bisa zargin satar naira miliyan goma daga wani kamfani, United Parcel Services, a yankin Gbagada na jihar Legas.

Ajayi, wanda aka gurfanar da shi a gaban majistare O Obasa, yana fuskantar tuhumar laifi ɗaya na sata wanda ƴan sanda suke tuhumar sa da shi. Rahoton The Punch

Kotun
Ma'aikaci Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Satar Kuɗin Kamfani Hoto: Punch
Asali: Twitter

Jami'an ɗan sanda Cletus Monjok, ya gayawa kotun cewa wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a yankin Meiran na jihar.

Kara karanta wannan

Ashsha Shiri Ya Ɓaci: An Cafke Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi, An Tura Shi Kotu

A cewar mai shigar da ƙarar laifin da ya aikata ya cancanci hukunci bisa sashin dokar aikata laifuka na 287(3) na jihar Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Takardar tuhumar da ake masa na cewa:

“Cewa kai, Folarin Ajayi, tsakanin shekarar 2021 zuwa watan Fabrairun 2023, a United Parcel Service, Gbagada, Legas, cikin gundumar Ikeja, ka saci tsabar kuɗi naira miliyan goma na kamfanin United Parcel Services."
"A dalilin hakan ka aikata laifi wanda ya saɓawa sashi na 200, da cancantar hukunci bisa sashin doka na 287 (3) na dokar laifukan jihar Legas ta shekarar 2015."

Sai dai, wanda ake ƙarar ya ƙi amsa laifin da ake tuhumar sa da shi.

Majistare E. Kubenje ta bayar da belin sa akan kuɗi naira dubu ɗari sannan da wasu mutane biyu da zasu tsaya masa.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Afrilun 2023 domin cigaba da shari'ar.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

A wani labarin na daban kuma, Festus Keyamo ya bayyana dalilin da ya sanya babi sunan sa cikin jerin lauyoyin da zasu kare Tinubu.

Festus Keyamo shine dai ƙaramin ministan kwadago da samar da ayyukan yi a gwamnatin shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng