"Sun Gaza Taimakon Kansu": Shehu Sani Ya Zolayi Gwamnonin G5 Bayan Shan Kayen Atiku

"Sun Gaza Taimakon Kansu": Shehu Sani Ya Zolayi Gwamnonin G5 Bayan Shan Kayen Atiku

  • Sanata Shehu Sani ya ce ba yadda za a yi gwamnonin G5 su iya taimakawa Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya
  • Sani ya ce yana da muhimmanci a lura cewa gwamnonin da Nyesome Wike na Ribas ya jagoranta sun gaza taimakawa kansu a siyasance idan aka duba zaben da ya gabata
  • A cewar tsohon dan majalisar, matasan Najeriya sun karbe mulki daga hannun tsaffin yan siyasa a sassan kasar

Tsohon dan majalisar jihar Kaduna wanda ya wakilci Kaduna Central ya zolayi gwamnonin G5 na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Sani a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter ya ce gwamnonin sun gaza ceton kansu a yayin babban zaben na 2023.

Gwamnonin na G5 sun hada da Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da Samuel Ortom na jihar Binuwai.

Kara karanta wannan

Zabukan Gwamnoni Na 2023: An Yi Hasashen Jerin Jihohin Da APC, PDP, Labour Party Ka Iya Lashewa

Shehu Sani da G5
Shehu Sani da gwamnonin G5. Photo: Shehu Sani, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Gwamnonin, a yayin da ake kololuwar kamfen din 2023 da zaben sun nuna bacin ransu ga shugabannin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin ta bakin jagoransu, Wike, sun yi kira ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP, ya yi abin da ya dace ta hanyar fada wa Iyorchia Ayu shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus.

Bayanai sun nuna cewa rikicin tsakanin gwamnoni da jam'iyyar ya samo asali ne bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP bayan nasarar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Sun kuma cika baki cewa Atiku ba zai ya cin zaben shugaban kasa na 2023 ba ba tare da taimakonsu ba.

Tsohon dan majalisan ya ce:

"Idan ma da G5 sun goyi bayan Atiku, ba zai yi wani banbanci ba. Ba su iya taimakon kansu ba balantana su taimaki dan takarar shugaban kasar."

Kara karanta wannan

Aiki ya kwabe: Cikin kowa ya duri ruwa, jiga-jigan PDP 10,000 sun koma APC a jihar Arewa

"Sun gaza fahimtar cewa talakawa sun dena karbar umurni daga wurin gwamna; gwamnonin yanzu roko su ke."

Ina nan daram-dam a jam'iyyar, Ayodele Fayose

Ayodele Fayose, jigon jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya karyata cewa ya fita daga jam'iyyar PDP.

Fayose ya yi karin bayani yana mai cewa yana nan daram-dam a PDP amma ya koma gefe guda ne don ya samu damar yin wasu maganganu a matsayinsa na dan kasa mai kishi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164