INEC Ta Cire Sunan Doguwa Daga Jerin Sunayen ’Yan Majalisun da Suka Ci Zabe
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta cire sunan Alhassan Ado Doguwa daga cikin zababbun ‘yan majalisu
- Ana zargin Ado Doguwa da hannu a mutuwa da raunata wasu mutane a Tudun Wada a ranar zaben 25 ga watan Faburairu
- Ya zuwa yanzu, bayan shafe kwanaki a magarkama, an sako dan majalisar tare da gindaya masa sharuddan da aka ce dole ya bi
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta cire sunan dan majalisar Kano, Alhassan Ado Doguwa daga cikin wadanda suka lashe zaben bana, Punch ta ruwaito.
A baya hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashen kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a jihar a zaben 25 ga watan Faburairu.
Baturen zabe na INEC, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai a baya ya ce, Doguwa na APC ya ci zabe da kuri’u 29,732, inda ya lallasa abokin mahayyarsa na NNPP mai kuri’u 34,798.
Babu sunan doguwa cikin zababbun ‘yan majalisu, ga dalili
Sai dai, a sabon jerin sunayen ‘yan majalisun da aka zaba, an nemi sunan Doguwa an rasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar hukumar, an tilastawa baturen zaben na INEC ne a lokacin da ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben.
A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da baturen zaben ke karanta sakamakon zaben jikinsa na rawa.
Yadda rikici ya barke bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Kano
Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, bayan barkwar rikicin da ya kai ga mutuwar wasu mutane a mazabar dan majalisar, an kwamushe shi tare da tasa keyarsa zuwa magarkama.
‘Yan sanda sun yi ikrarin cewa, ta sanadiyyar Doguwa an hallaka wasu mutum uku tare da jikkata wasu da basu ji ba basu gani ba a hedkwatar kamfen NNPP da ke Tudun Wada.
Hakazalika, sun ce an kone wasu mutum biyu da ransu duk da hannun dan majalisar na jam’iyyar APC.
An yi belin Doguwa
Bayan wannan ne aka tasa keyarsa zuwa magarkama, inda ya shafe kwanaki biyar a daure, kana daga baya alkalin kotun majistare ya ba da belinsa da sharudda.
Hakazalika, an hana Doguwa zuwa mazabarsa a lokacin zaben gwamna da ke tafe a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.
Asali: Legit.ng