Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindiga Sun Ceto Mutum 23 a Jihar Kaduna

Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindiga Sun Ceto Mutum 23 a Jihar Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar wasu miyagun ƴan bindiga a jihar Kaduna
  • Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar tare da haɗin guiwar ƴan sakai waɗanda suka yi musu rakiya
  • Sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mutane da ƴan bindigar suka sace a yayin wani hari da suka kai

Jihar Kaduna- Dakarun sojoji sun samu nasarar fatattakar wasu ƴan bindiga sannan suka ceto wasu mutum ashirin da uku da aka sace a ƙauyen Dogon Daji cikin ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

A ranar Juma'a 3 ga watan Maris, 2023 ƴan bindiga suka farmaki Dogon Daji, inda suka halaka mutum ɗaya sannan suka sace wasu mutum ashirin da uku.

Sojoji
Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindiga Sun Ceto Mutum 23 a Jihar Kaduna Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Danmalam Usman, wanda ɗan'uwan sa yana ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da ceton su da akayi ga ma'aikacin Daily Trust a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa sojojin sun samu rakiyar ƴan sakai daga Jere da Kagarko, inda suka dira a cikin sansanin ƴan bindigar wanda yake a cikin dajin dake tsakani da Jere da Kagarko, a ranar Lahadi inda suka yi musayar wuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa fitar da sojojin suka yi ta haifar da nasara inda suka fatattake su sannan suka ceto mutum ashirin da uku.

Ya kuma ƙara da cewa an kai mutanen da aka ceto ɗin zuwa ofishin ƴan sanda na Jere inda aka haɗa su da ƴan'uwan su.

Wata majiya a ofishin ƴan sanda na Jere ya tabbatar da ceto mutanen da akayi.

Malama Samaila Babangida, Madakin Janjala, wani ƙauye mai makwabataka da su, ya tabbatar da ceto mutanen da aka sace.

Ya bayyana cewa:

“Muna fatan muma sojoji za su kawo mana ɗauki a nan Janjala domin ceto wasu daga cikin mutanen mu da ƴan bindiga suka sace.

Wani Soja Ya Bindige Oga, Ya Harbe Abokin Aikinsa, Sannan Ya Kashe Kan Shi

A wani labarin na daban kuma wani soja ya tafka wata ta'asa a jihar Sokoto. Sojan ya bindige ogan sa sannan ya haɗa da wasu abokan aikin sa.

Daga baya kuma sai ya halaka kan sa da kan sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng