Wani Ɗan Sanda Ya Rasa Ransa a Gidan Tsohon Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Ogun

Wani Ɗan Sanda Ya Rasa Ransa a Gidan Tsohon Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Ogun

  • Idan ajali yayi kira to ko babu cewa a je, hakan ya faru da wani jami'in ɗan sanda wanda ya rigamu gidan gaskiya a jihar Ogun
  • Jami'in ɗan sandan ya mutu lokacin da yake tsaka da aikin sa a gidan tsohon kwamishinan ƴan sandan jihar
  • Ba a bayyyana takamaiman abinda yayi silar mutuwar sa ba, sai dai an tabbatar da ya kwanta barci ne wanda bai farka daga shi ba

Jihar Ogun- Wani jami'in ɗan sanda ya rasa ransa a gidan tsohon kwamishinan ƴan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole, a ƙarshen mako.

Ɗan sandan mai suna Sgt Gbenga Onakomaya, ya mutu ne a ranar Asabar a gidan Bankole wanda yake a rukunin gidaje na Kemta, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Yan sanda
Wani Ɗan Sanda Ya Rasa Ransa a Gidan Tsohon Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Ogun Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Wakilin Daily Trust ya samo cewa ɗan sandan wanda yake aikin gadi a gidan tsohon kwamishinan, ya kwanta barcin da bai farka ba.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Takarar Gwamna da Wasu 9 Ruwa a Jallo

An garzaya da shi zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya dake a Idi Aba, cikin birnin Abeokuta, inda likitan dake a bakin aiki ya tabbatar da ya rigamu gidan gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta bayyana cewa an ajiye gawar ɗan sandan a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin. Rahoton Daily Post

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana a matsayin ƙarar kwanan.

A kalamansa:

"Wani jami'in ɗan sanda ya tafi wajen aiki, ya kwanta barci amma bai tashi ba da safe."
"Lamari ne na zuwan mutuwa kwatsam. Ba wani abu bane wanda ba a saba gani ba. Ba wani abu bane wanda bai taɓa faruwa ba. Kowa zai iya rashin lafiya ya rasu a ko ina ne, ko da a cikin gida ne."

Duka ba a fi wata ɗaya ba da sauyawa Bankole wajen aiki daga jihar Ogun, inda aka musanya shi da tsohon kakakin rundunar ƴan sanda, Frank Mba.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

Wani Soja Ya Bindige Oga, Ya Harbe Abokin Aikinsa, Sannan Ya Kashe Kan Shi

A wani labarin na daban kuma, wani soja ya halaka kansa bayan ya bindige oga da abokin aikin sa har lahira.

Lamarin dai ya faru ne a jihar Sokoto dake a Arewacin Najeriya. Tuni dai aka fara gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng