Wani Soja Ya Bindige Oga, Ya Harbe Abokin Aikinsa, Sannan Ya Kashe Kan Shi
- Rundunar sojojin Najeriya ta bada sanarwa wasu sojoji a filin daga a yankin Rabah a jihar Sokoto
- Wani kurtun sojan kasa ake zargin ya harbe uban gidansa da abokin aikinsa, kuma ya kashe kan shi
- A halin yanzu jami’an sojojin su na barzahu, kwamiti zai yi bincike domin ya gano abin da ya faru
Abuja - A ranar Litinin, Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da wani mummunan lamari wanda ya auku a bakin aiki a garin Rabah da ke jihar Sokoto.
Jaridar nan ta The Sun ta ce an tabbatar da mutuwar wasu sojoji biyu a sakamakon harbi da abokin aikinsu ya yi masu a ranar Lahadin nan da ta wuce.
Birgediya Janar Onyema Nwachukwu wanda shi ne Darektan hulda da jama’a na gidan sojan kasa, ya bada wannan sanarwa jiya a babban birnin Abuja.
Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya
Har zuwa lokacin da ya fitar da jawabi a jiya, Janar Onyema Nwachukwu ya ce ba a gano ainihin abin da ya jawo kurtun sojan ya jawo asarar rayuka ba.
GOC ya je ya yi ta'aziyya
Darektan ya ce Shugaban dakarun hadin-gwiwa da Hadarin Daji a yankin kuma GOC na runduna ta takwas, Manjo Janar Godwin Mutkut ya ziyarci wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika wasu manyan jami’an sojoji sun kai ziyara zuwa inda abin ya faru, kuma sun yi wa rundunar ta’aziyyar wannan mummunan rashi da aka yi.
Daily Trust ta ce Janar Godwin Mutkut ya yi kira ga sojojin su zama masu hadin-kai da son juna.
An kafa wani kwamiti na musamman da zai yi aiki domin gano abin da ya jawo faruwar wannan masifa, kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a dazu.
Kiran da Janar Godwin Mutkut ya yi
“Ya yi kira a gare su da su zama ‘yanuwan juna, su rika kai karar duk wani haka-da-haka da aka gani domin gudun sake faruwar hakan.
Sannan ya karfafe su da su kwantar da hankalinsu, kuma su cigaba da kokari wajen aikinsu.
Gidan soja yana mai matukar damuwa da wannan mummunan lamari da ya auku, kuma an kafa kwamitin BOI domin gudanar da bincike.
Ana sa ran cewa sakamakon binciken kwamitin na BOI zai taimaka wajen kawo karshen irin wadannan abubuwa a nan gaba.
- Janar Onyema Nwachukwu
Satar kudin fansho
Rahoton da aka fitar a baya ya bayyana cewa shari’ar Hukumar EFCC da Garba Abdullahi Tahir ta haifar da daurin shekaru fiye da 20 a kurkuku.
Inyang Ekwo mai shari’a a kotun tarayya da ke garin Abuja ya samu tsohon Akantan ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin da satar fanshon jama'a.
Asali: Legit.ng