Alkali Ya Yankewa Akanta Hukuncin Daurin Shekaru 21 Saboda Cin Kudin Fansho

Alkali Ya Yankewa Akanta Hukuncin Daurin Shekaru 21 Saboda Cin Kudin Fansho

  • Bayan tsawon lokaci ana fafatawa a kotu, Hukumar EFCC tayi nasarar daure Garba Abdullahi Tahir
  • Alkalin kotun tarayya mai zama a Abuja ya samu tsohon Akanta da laifin wawuran fanshon ma’aikata
  • Inyang Ekwo ya gamsu da hujjojin EFCC, ya samu Garba Tahir da satar N26m na wadanda suka yi ritaya

Abuja - Wani tsohon Akanta a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Garba Abdullahi Tahir zai yi zama a gidan gyaran hali.

Tashar talabijin Channels ta rahoto cewa an yankewa Garba Abdullahi Tahir hukuncin daurin shekaru 21 saboda laifin satar miliyoyi.

An samu wannan tsohon ma’aikaci da aka fi sani da Tahir Garba da hannu wajen satar Naira miliyan 26.1 na masu karbar fansho a kasar.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gurfanar da Garba Tahir a babban kotun tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Hukumar EFCC ta je kotu

Rahoton ya ce EFCC ta tuhumi tsohon jami’in da laifuffuka bakwai da suka hada da satar kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka gurfanar da shi a kotu, lauyan gwamnati ya jefi wannan tsohon ma’aikacin gwamnatin tarayya da laifin wawurar N7.8m tun 2010.

Gidan yari
Gidan yarin Kuje Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

EFCC ta ce Garba Abdullahi Tahir ya tura wannan kudi zuwa asusun wani kamfanin canjin kudi mai suna CHARO Bureau de Change Ltd.

Wannan laifi ya sabawa sashe 14 (1) (a) na dokar safarar kudi ta shekarar 2004 kuma wanda ake tuhuma ya musanya zargin da ake yi masa.

A karshe lauyan hukumar binciken na EFCC ya gabatar da hujjoji da shaidu da ke tabbatar da Garba Tahir ya yi sama da fadi da dukiyar.

Ranar wanka ba a boye cibiya

Jaridar Independent ta ce a ranar Juma’ar da ta gabata, Mai shari’a Inyang Ekwo ya zartar da hukuncin dauri yana mai gaskata gwamnati.

Kara karanta wannan

Jihohi 6 Sun Dumfari Babban Kotun Najeriya, Sun Huro Wuta a Soke Zaben Shugaban Kasa

Alkali Inyang Ekwo ya gamsu cewa wanda ake zargi ya aikata duka laifuffukan nan bakwai, ya yanke masa hukuncin daurin shekaru uku.

Kowane laifi yana da ukubar daurin shekaru wanda za su yi aiki a kan Garba Tahir a lokaci guda.

Kotun koli ta gama magana

A hukuncin da kotun koli ta zartar a game da batun sauya takardun kudi, an ji labari cewa Alkalai sun ba jihohi gaskiya a kan Gwamnatin tarayya.

Alkali Inyang Okoro ya ce canza kudi ya saba kundin tsarin mulki kuma an tauye hakkin Jihohi. Lauyan gwamnati ya gamsu da wannan kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng