Shugaban APC Na Cross River Ya Marawa Dan Takarar Majalisar Dokoki a LP Baya
- Dan takarar majalisa na jam’iyyar Labour a jihar Cross River ya hada kai da shugaban jam’iyyar APC gabanin zaben ranar Asabar 11 ga watan Maris
- Shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce, wannan hadi zai taimakawa jam’iyyun biyu wajen cimma manufarsu
- Jam’iyyar Labour a jihar ta bayyana bacin ranta da yadda dan takararta ya kusance jam’iyyar ta APC mai mulkin kasa
Jihar Cross River - A wani yanayi mai daukar hankali, shugaban jam’iyyar APC a jihar Cross River, Barista Alphonsus Ogar Eba ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar majalisa na Labour a jihar, Mr Brian Odey.
A cewarsa, tun a baya suna da alaka mai karfi da alkawari a tsakaninsu da dan takarar na majalisa a mazabar Yala-1, kuma dole ya cika a yanzu, inji rahoton Tribune Online.
A jawabin shugaban na APC, ‘yan jam’iyyar Labour da mabiyansu da kuma ‘yan APC duk suna da buri daya; kawo shugaban kasa daga yankin Kudu.
Ogar, wanda aka ce ya jima yana tattaunawa da jam’iyyar Labour tun kafin zaben shugaban kasa, ya kuma ce bai san wani dan takarar gwamna na Labour ba a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dan takarar Labour ya magantu
Da yake kawar da shakku kan alakarsa da shugaban na APC, dan takarar jam’iyyar Labour da ake magana a akansa, Brian Odey ya ce:
“Ina mai matukar farin cikin cewa jam’iyyar kasa kamar APC za ta mara min baya, kuma ina son tabbatarwa jam’iyyar cewa, karamar hukumar Yala za ta zabe ta.
“Ina son wannan babbar jam’iyya (APC) ta mara min baya kan abin da nake son yi da kuma aiki a kai. APC ba ta da dan takara a wannan kujerar, don haka ba wata matsala bace don ta mara min baya.”
Jam'iyyar Labour ta fusata
Sai dai, matakin jiha na jam’iyyar Labour a Cross River ya yi Allah wadai da wannan gami na APC da dan takararta, Vanguard ta ruwaito.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Lekan Ofem ya yi gargadin cewa, jam’iyyar na da dan takarar gwamna mai suna Ogar Osim kuma ya kamata dan takarar majalisan ya nesanta kansa da APC.
A bangare guda, dan takarar gwamnan jam’iyyar Labour a jihar Adamawa ya bayyana janyewa tare da marawa ‘yar takarar gwamnan APC, Sanata Aishatu Ahmed Binani.
Asali: Legit.ng