Bankuna Sun Ci Gaba da Baiwa Mutane Takardun N500 da N1000
- Wasu bankunan kasuwanci a Abuja da Kano sun fara bayar da tsoffin takardun N500 da N1000 yau Litinin
- Hakan na zuwa ne bayan Kotun koli ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin tsarin CBN na sauya naira a Najeriya
- Bincike ya nuna da yawan rassan wasu bankunan N200 kadai suke bayarwa, suna jiran umarni
Bayan hukuncin Kotun Koli na tsawaita wa'adin amfani da tsoffin naira, wasu bankunan kasuwanci sun fara baiwa kwastomominsu tsofffin naira N500 da N1000.
Aƙalla bankuna uku ne a birnin tarayya Abuja suka fara biyan mutane da tsohon takardan N1000 da N500 ranar Litini yayin wani banki ɗaya tal a Kano ya bi sahun su.
Binciken da Daily Trust ta gudanar yau Litinin 6 ga watan Maris, 2023 ya nuna cewa da yawan bankuna na nan kan bakarsu na baiwa mutane tsohuwar N200 kacal.
Wasu rassan bankin Guaranty Trust watau GT sun fara biyan mutane da tsohon naira a birnin tarayya, amma wasu bankunan kamar Polaris a Abuja ba su fara ba kawo yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ma'aikacin banki ya ce har yanzun N200 kacal su ke bayarwa a Polaris, "Saboda kawo yanzu bamu samu umarni kan abinda ya dace mu yi ba."
A ɗaya bangaren, wata majiya daga GT Bank ta ce masu ruwa da tsakin bankin ne suka umarci su biya kwastomomi da tsoffin kuɗin a kan kanta.
"Matsala ɗaya ce ba zasu karbi tsoffin naira daga kwastomomi ba har sai sun cike Fam ɗin CBN, babu wani umarni game da haka daga sama," inji shi.
Har kawo yanzun da muke haɗa wannan rahoton, Legit.ng Hausa ba ta samu tabbacin ko CBN ya fitar da sabon jadawalin da kowane banki zai bi umarnin da ke ciki ba, Sahara Reporter ta rahoto
Masana tattalin arziki a Najeriya sun roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bi hukuncin Kotu na tsawaita wa'adin tsoffin kuɗi.
Legit.ng Hausa ta tuntubi wani ma'aikacin GT Bank a jihar Katsina kan wannan ci gaban, ya ce har yanzun suna dakon umarni daga CBN kafin su fara biya.
Ma'aikacin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya shaida wa wakilin mu cewa duk bankin da ya fara biyan tsohon kuɗin, to ya tara ne ya rasa yadda zai yi da su.
Ya ce:
"Mu nan a GT reshen Katsina bamu bayarwa, amma wani reshen Sterling sun raba wa mutane daga baya kowa ya maida masu, a zahirin gaskiya Buhari ne kaɗai zai ce a karba nan take a ci gaba da karɓa."
"Bankuna da yawa sun shiga matsala a baya, sun karbi tsohon naira bayan 10 ga watan Fabrairu, CBN ya titsiyesu, to ina tsammanin irin rassan ne da dama neman kai suke da kuɗin, shiyasa suka fara baiwa mutane."
CBN Ya Yi Gum Game da Hukuncin da Ƙotun Koli Ta Yanke Kan Sauya Naira
A ɗaya gefen, wani ma'aikacin babban bankin Najeriya (CBN) ya yi karin haske biyo bayan hukuncin da Kotun koli ta yanke
Har kawo yanzun ana dakon jin matakin da CBN zai ɗauka kan tsawaita amfanu da takardun tsohon naira da Kotu ta yi a hukumance amma bai ce komai ba.
Asali: Legit.ng