Hotunan Yadda Atiku, Ayu da Tambuwal Suka Jagoranci Zanga-Zangar a Ofishin INEC
- Jam’iyyar PDP ta fito domin nuna adawa da yadda ta sha kaye a zaben shugaban kasa da aka yi kwanan nan
- Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan PDP ne suka bayyana a helkwatar INEC
- A tun farko, Bola Tinubu na APC ne ya ci zabe a Najeriya, amma PDP ta ce sam bata amince da sakamakon zaben ba
FCT, Abuja - Hotuna sun yadu a kafar sada zumunta na yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya jagoranci zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben shugaban nasa na 2023.
Atiku Abubakar na tare da sauran jiga-jigan PDP, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Ayu Iyorchia da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a helkwatan INEC da Abuja.
Sauran wadanda ke cikin zanga-zangar sun hada da; shugaban kwamitin kamfen na PDP, kuma gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel da dai sauran manyan masu fada a ji a jam'iyyar.
A tun farko, dan takarar na PDP ya ce bai amince da sakamakon zaben shugaban kasan da ya kawo Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
PDP da dan takarar sun zargi almundahana da siyan kuri’u a lokacin zaben na shugaban kasa da aka gudanar, rahoton Channels Tv.
Zanga-zanga ta barke a Abuja
Wannan ne yasa suka shirya gagarumin zanga-zanga don nuna fushinsu da kuma neman a soke zaben da aka gudanar a karshen makon jiya.
A hotunan da muka gani, an ga lokacin da jiga-jigan PDP da mabiya jam’iyyar a cikin motoci sanye da bakaken kaya suna karade titunan da ke zagaye da helkwatar INEC.
Kalli hotunan, kamar yadda The Nation ta yada:
Kotu ya ce Atiku da Obi za su iya duba kayan aikin INEC
A wani labarin kuma, kun ji yadda kotun koli ya ba ‘yan takarar shugaban kasa a LP da PDP damar duba kayan aikin zabe.
Wannan na zuwa ne bayan da suka bayyana rashin amincewa da sakamakon da aka fitar a kwanakin baya.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana kan sakamakon zaben da ya kawo Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng