Allah Bai Halicci Najeriya Don Ta Kare a Cikin Tsiya da Fatara Ba, Inji Tsohon Shugaba Obasanjo

Allah Bai Halicci Najeriya Don Ta Kare a Cikin Tsiya da Fatara Ba, Inji Tsohon Shugaba Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana manufar Allah game da kasar da kuma al’ummar cikinta
  • Tsohon shugaban ya bayyana cewa, Allah bai halicci Najeriya don ta zama matsiyaciyar kasa ba, shugabanninta ne suka lalata ta
  • A taron cikarsa shekaru 86 a duniya, Obasanjo ya ce bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai, su yi addu’a tare da tabbatar da taken cewa Najeriya ce uwa a Afrika

Jihar Ogun - Tsohon shugaban Najeriya ya bayyana cewa, Allah ya halicci Najeriya da fata mai kyau, amma aka samu akasi daga masu tafiyar da lamurranta.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi 5 ga watan Maris 2023 yayin taron cikarsa shekaru 86 a duniya, jaridar Punch ta ruwaito.

A jiya Lahadi ne aka yi bikin nasa, kuma an yi ne a gidansa ne Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a Kudu masu Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Sanata ya fadi wulakacin da gwamnan CBN zai gani bayan saukar Buhari

Obasanjo ya fadi manufar samar da Najeriya
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

A cewarsa, Allah bai halicci kasar don ta zama matsiyaciya ba, inda yace baragurbin shugabanni da aka samu a kasar ne suka lalata komai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obasanjo ya fadi fadin shirin ubangiji game da Najeriya

Ya bayyana cewa, abin kokawa ne yadda Najeriya ta gaza daukar haske game da kimiyya da fasaha wajen zama mai iya rike kanta ta fannin abinci, rahoton People's Gazette.

A kalamansa:

“Allah ya halicci Najeriya ne da manufa mai girma.
“Ba wai kawai mun gaza zama manya a cikin rana ba, ba mu kasance babbar kasa a Afrika ba. Wasu na kiranmu amma masu laka a kafa.”

Ba wannan ne karon farko da Obasanjo ke yin magana game da halin da Najeriya ke ciki ba, ya sha bayyana rashin amincewa da jin dadinsa da yadda kasar ke komawa baya.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

Sai dai, Obasanjo na daga cikin shugabannin Najeriya, kuma a kansa ne aka fara mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, inda ya shafe shekaru takwas yana jan ragamar kasar.

Obasanjo ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023

A bangare guda, Obasanjo ya ce sam bai kamata a yi amfani da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya ba a bana.

Ya bayyana cewa, akwai bukatar soke zaben don a ceto ‘yan Najeriya daga hadarin da ka iya faruwa a nan kusa.

A tun farko, Obasanjo ya kasance mai goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.