Da dumi-dumi: An Harbe Wani Basarake Har Lahira a Jihar Kano

Da dumi-dumi: An Harbe Wani Basarake Har Lahira a Jihar Kano

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun harbe dagacin kauyen Maigari har lahira a karamar hukumar Rimin Gado, Kano
  • Shugaban karamar hukumar Rimin Gado, wanda ɗa ne ga mamacin, Munir Dahiru Maigari, ya ce lamarin ya faru da daddare
  • Ya ce a halin yanzu suna shirye-shirye yi masa Jana'iza kamar yadda addini ya umarta kuma ba zai ce komai game da lamarin ba a yanzu

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an harbe Dagacin ƙauyen Maigari, da ke ƙaramar hukumar Rimin Gado, a jihar Kano, Dahiru Abba, kuma Allah ya masa rasuwa.

Ɗan marigayin kuma shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, Barista Munir Dahiru Maigari, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

Dahiru Abba
Dagacin garin Maigari, Dahiru Abba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Maigari ya ce, "Lamarin ya faru da misalin karfe 2:00 na dare, sun kutsa kai kuma suka aiwatar da kudirinsu, yanzu haka muna shirye-shiryen yi masa jana'iza."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Ciki Fada, Sun Yi Garkuwa da Matan Sarki 2 da Ɗansa a Jihar Arewa

"Ba zamu ce komai ba dangane da makasudin kashe shi a halin yanzu, amma tabbas ya rasu kuma muna Addu'a Allah ya masa rahama."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa yan bindigan sun kutsa cikin gidan Basaraken, suka ci masa mutunci daga bisani suka bude wuta.

Ya kuma ƙara da bayanin cewa za'a yi wa mamacin jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a gudansa da ke ƙauyen Maigari, ranar Lahadi da safe.

Yayin da aka tuntube shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a halin yanzun bai samu labarin faruwar lamarin ba.

Kiyawa ya ƙara da cewa zai bincika ya gano ainihin abinda ya faru kafin ya yi magana da manema labarai, kamar yadda Punch ta ruwaito.

'Yan Boko Haram Sama da 1000 Sun Mika Wuya

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

A wani labarin kuma mayakan Boko Haram da yawa sun miƙa wuya bayan yan ISWAP sun sheƙa sama da yan ta'adda 200

Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya ta ce sun miƙa wuya ne sakamakon rashin mafaka yayin da abokin faɗansu ISWAP ke nemansu ta kashe a yankunan Borno.

Bayanai sun nuna cewa a ranakun 26 da 27 ga watan Fabrairu, an yi kazamin artabu tsakanin ƙungiyoyin yan ta'addan guda biyu kuma da yawa sun sheƙa lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262