Shugaba Buhari Ya Sauka a Doha, Babban Birnin Kasar Qatar

Shugaba Buhari Ya Sauka a Doha, Babban Birnin Kasar Qatar

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka a babban birnin Qatar watau Doha da yammacin ranar Asabar din nan da muke ciki
  • Mai taimakawa shugaban kan harkokin kafafen watsa labarak ya ce Buhari zai halarci ƙasashe masu tasowa karo na 5
  • Mallam Garba Shehu ya ce Buhari ya tafi Doha ne domin amsa gayyatar Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani

Shugaban ƙasa, Alhaji Muhammadu Buhari, ya isa Doha, babban birnin ƙasar Qatar da daren Asabar din nan domin halartar taron kasashe masu tasowa karo na 5.

Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin kafafen watsa labarai, Buhari Sallau, ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari na sauko wa daga jirgi a Doha Hoto: BuhariSallau1
Asali: Twitter

Mista Sallau ya wallafa a shafinsa cewa:

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sauka a Doha, ƙasar Qatar gabanin fara taron majalisar dinkin duniya kan kasashe masu tasowa karo na 5 ranar 4 ga watan Maris, 2023."

Kara karanta wannan

Manyan Yan Siyasan Arewa 11 Suka Taba Kasa A Zaben 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan shi ne karo na hudu da shugaban kasa Buhari ya yi tafiya zuwa ƙasar waje a cikin shekarar nan 2023.

A sanarwar farko da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar, ya ce Buhari zai tsunduma wannan tafiya ne domin amsa gayyatar Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.

A cewar Shehu, Buhari da sauran takwarorinsa daga sassan duniya zasu taru a Qatar tsakanin 5 zuwa 9 ga watan Maris, 2023.

Wannan taron na zuwa ne watanni Shida bayan gwamnatin Qatar ta hana ziyarar Buhari ta baya da aka tsara ranakun 11 da 12 ga watan Satumba, 2022 saboda ranakun ba su dace ba.

Ofishin jakadancin Qatar a nan Najeriya ya rubuta wa ma'aikatan harkokin kasashen waje, inda ya bayyana cewa lokacin da aka zaɓa na ziyarar bau dace da lokutna da Al Thani ke da su ba.

Kara karanta wannan

Allah ya sa: Buhari ya yiwa 'yan Najeriya alkawari mai zafi, zai cika kafin ya sauka mulki

Jam'iyyar PDP Ta Karyata Jita-Jitar Gwamna Adeleke Zai Koma APC

A wani labarin kuma jam'iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo a soshiyal midiya cewa gwamnan Osun na shirin sauya sheka zuwa APC.

A wata sanarwa da shugaban PDP na Osun ya fitar, ya ce labarin kirararre da aka tsara domin ɗauke wa mazauna Osun hankali kar su zabi wanda ya dace da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262