Gwamna Badaru Ya Bada Sandan Sarauta Ga Sabon Sarkin Masarautar Dutse

Gwamna Badaru Ya Bada Sandan Sarauta Ga Sabon Sarkin Masarautar Dutse

  • Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, gwamnan jihar Jigawa ya gabatar da sandan sarauta ga sabon sarkin masarautar Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi
  • Manyan sarakuna da jami'an gwamnati da yan siyasa daga Jigawa da sauran sassan Najeriya sun halarci bikin ba da sandan da aka yi a ranar Asabar, a Dutse
  • Sabon sarkin, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya gode wa wadanda suka halarci taron ya kuma yi alkawarin dora ayyuka da mahaifinsa marigayin sarki ke yi

Jihar Jigawa - Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya ba da sandan sarauta ga sabon Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, Daily Trust ta rahoto.

Dubban mutane da dama da masu fatan alheri a Jigawa da jihohi da ke makwabta sun halarci taron da aka yi a Aminu Kano Tri-Angle, Dutse, a ranar Asabar 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Yan Boko Haram Sama Da 200 a Borno

Sarkin Dutse
Bikin mika sandan sarauta ga sabon sarkin Dutse. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru ya ce kujerar sarautar gadon mahaifinsa ne.

Gwamnan ya kara da cewa:

"Muna baka shawara ka yi koyi da halayen mahaifin ka da jagoranci nagari."

Ya yi addu'a ga marigayin Sarkin Dutse Dr Nuhu Muhammad Sunusi, saboda tausayinsa da jagoranci na gari a lokacin rayuwarsa ya kuma yi addu'a Allah ya saka masa da aljanna.

Wasu cikin manyan baki da suka halarci bikin ba da sandan sarautan sabon sarkin Jigawa

Gwamnan ya mika godiya ga wasu manyan baki da suka halarci bikin kamar Sarkin Musulmi Alh. Sa’ad Abubakar III, zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shatima, tsohon gwamnan Jigawa, Dr. Sule Lamido, gwamnan Plateau, Simon Bako Lalong, Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero, sarakunan Ringim, Hadejia, Gumel, Kazaure da Zazzau, Kaltingo, Zuru, Bauchi, da sauransu.

Zan dora daga inda mahaifina ya tsaya, Sabon Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi

Kara karanta wannan

Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa

A jawabinsa, sabon sarkin na Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, ya bukaci mutane su taya shi addu'a Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ke kansa bisa tsoron Allah.

Ya yi alkawarin yin adalci da cigaba da ayyuka na gari da mahaifinsa ya yi.

Ya ce:

"Zan ci gaba da ayyukan da mahaifina ya bari kuma zan yi iya kokarina don ganin cewa duk kyawawan abubuwan da mahaifina marigayi sarki ya yi za su cigaba har da karawa."

Sunusi ya ce zai ziyarci dukkan yankunan da ke karkashinsa don raba sadaka ga talakawa.

Ya kara da cewa:

"Zan cigaba da rarraba sadaka da mahaifina ya tattara kuma in cigaba aikin na ta hanyar amfani da masu karbar sadakan."

Sarkin ya mika godiya ga manyan mutane da suka halarci taron da sauran masu fatan alheri.

A baya kun ji cewa Gwamna Muhammad Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ya amince da nadin Alhaji Hameem Muhammad Sunusi a matsayin sabon sarkin Dutse.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Basarake A Jigawa Da Yaransa 3 Sun Mutu A Hadarin Mota

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164