Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matan Wani Basarake a Jihar Taraba
- Yan bindiga sun kutsa har cikin gidan Basarake a Sarkin Kudu, jihar Taraba, sun yi awon gaba da matansa biyu da ɗa ɗaya
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun kai hari gidan ne yayin da Basaraken ya yi tafiya ya bar gida ranar Jumu'a da daddare
- Rundunar 'yan sanda ta ce tuni ta fara bincike kuma jami'ai sun cafke wasu da ake zargin suna da alaƙa da harin
Taraba - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da mata biyu a ɗan Basaraken garin Sarkin Kudu da ke jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne ranar Jumu'a da daddare lokacin da maharan suka kutsa kai cikin fadar Sarkin da ke ƙaramar hukumar Ibbi.
Bayanai sun nuna cewa basaraken mai suna, Dansalama Adamu, ya yi tafiya ya bar yankin masarautarsa lokacin da 'yan bindigan suka shiga suka sace iyalansa.
Har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton, babu wanda ya san inda maharan suka yi da matan biyu da ɗan Basaraken ba kuma ba su tuntuɓi ko mutum ɗaya daga cikin iyalansa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Bugu da ƙari, kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa jami'ai sun damƙe wasu da ake zargin suna da hannu a garkuwa da iyalan Basaraken.
DSP Abdullahi ya ƙara da cewa a halin yanzun dakaru sun matsa kaimi wajen ganin sun kubutar da iyalan basaraken cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce waɗanda aka kama da zargin hannu a lamarin sun yi bayani masu matuƙar muhimmanci da zai taimakawa yan sanda wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya
A wani labarin kuma Yan bindiga sun kaiwa ayarin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC hari a jihar Enugu
Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce lamarin ya faru ne a garin Agbani kuma da zuwan maharan suka bude wa motar da yake ciki wuta.
Asali: Legit.ng