Tirkashi: Jim Kadan da Yin Zabe Bankuna na Cigaba da Amsar Tsofaffin N500 da N1000

Tirkashi: Jim Kadan da Yin Zabe Bankuna na Cigaba da Amsar Tsofaffin N500 da N1000

  • Biyo Bayan Hattama Zaben Shugaban Kasa Dana Yan Majalisu Yanzu haka Bankuna sun dawo Amsar Tsofaffin Kuɗaɗen N500 da N1000
  • Jerin Bankunan da suke Amsar Tsofaffin Kuɗaɗen Sun Haɗa da GTB, First Bank, da kuma Fidelity Bank.
  • Hakan na Zuwa ne a Dai-dai Lokacin Shafin da CBN Ya Bude Domin Cike Buƙatar Canja Kuɗin Yake a Buɗe.

Bankunan Kasuwanci a Najeriya na cigaba da yin hada hadar amsar tsofaffin kuɗaɗe, lokaci ƙadan bayan kammala zaɓukan shugaban ƙasa dana ƴan majalisun dokokin da tarayya.

Canja fasalin na kuɗin yazo ne a lokacin da ƴan ƙasa da siyasa suke ƙoƙarin ganin sun samu abinda zasu gudanar da al'amuran su na rayuwa dashi. Abinda yasa aka samu kiki-kaka a kowani sashi na rayuwa.

To saidai yin kunnen uwar shegu da bankunan sukayi na ƙin daina amsar tsofaffin kuɗin yayi hannun riga da bayanin da CBN yayi akan lamarin.

Kara karanta wannan

Kada Ka Kuskura Ka Haɗa Gwamnatin Haɗaka Inji Tanko Yakasai Ga Tinubu

getty
Tirkashi: Jim Kadan da Yin Zabe Bankuna na Cigaba da Amsar Tsofaffin N500 da N1000 Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bankin ya nace akan cewa bai bada umarni ga bankuna suci gaba da amsar Tsofaffin Kuɗaɗe a hannun mutane ba. Musamman na tsofaffin N500 dana N1000.

Jerin Bankunan da suke Amsar Tsofaffin Kuɗaɗen

Bincike ya nuna cewa wanɗannan sune jerin bankunan da suke amsar tsofaffin kuɗaɗe, kama daga GTB, First Bank, sai kuma Fidelity Bank.

Sashin da aka buɗe domin maida tsofaffin kuɗaɗen ya ruwaito cewar, mutane masu kuɗi N500,000 zuwa ƙasa ne zasu iya zuwa bankunan suyi wannan ajiyar.

Legit NG Ta Duba Shafin Yanar Gizo Gizo da CBN Ya Bude Domin Samun Tabbaci.

Binciken da Jaridar Legit NG ta gabatar ya nuna cewa har yanzu shafin na CBN a bude yake.

Kuma shafin ya bada umarni kamar haka:

A danna nan domin shiga shafin

Kara karanta wannan

Yan Watanni Bayan Rabuwa Da Matarsa Da Kuma Musulunta, JJC Skillz Yayi Aure A Kano

https://crs.cbn.gov.ng

Jaridar Legit NG ta kuma ruwaito cewar, wani babban jami'i a CBN yace, jita jita ce kawai amma CBN ne yabada umarnin amsar tsofaffin kuɗaɗen na N500 da N1000.

Inda yace sai dai CBN ɗin yace, mafi yawan abinda za'a iya amsa a wajen mutum bazai wuce N500,000 ba.

To amma duk da wannan tabbacin, CBN ya ƙaryata batun ta hannun tsohon jami'in ta na daraktan sadarwa Osita Nwanisiobi.

Amma kafin karyatawar, umarnin amsar tsofaffin kuɗin na 500 da 1000 yana kan shafin yanar gizo gizo ta bankin.

Bututun Mai Ya Kama Da Wuta A Rivers, Ya Hallaka Gomman Barayin Danyen Mai

Ana bikin duniya ake na kiyama, an samu gobara a jihar Rivers, yayin da wasu barayi suka ɗimfari wajen ɗan yen mai domin su ɗibi ganima.

Gobarar dai ta auku ne da misalin ƙarfe 2 na daren Juma'a yayin da wani direban ya tayar da ɗaya daga cikin motocin da ake amfani wajen satar ɗanyen man.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Jam'iyyar Kwankwaso Tayi Kira a Soke Zaɓen Shugaban Kasa, Ta Bayyana Dalilan Ta

Ana amfani da motar ne wajen tafiyar da man sata zuwa cibiyoyin tace danyen mai na bayan fagge.

Motoci da rayuwa da yawan ne suka samu mutuwa da lalacewa kamar yadda Jaridar Legit.ng ta ruwaito yau da safiyar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida