Yau Take Ranar Yanke Hukunci Akan Canja Fasalin Naira Da Hana Kudi Zurga-Zurga

Yau Take Ranar Yanke Hukunci Akan Canja Fasalin Naira Da Hana Kudi Zurga-Zurga

  • Jihohin Kaduna, Kogi, Zamfara, Katsina, Lagos, Cross River, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Rivers, Kano, Niger, Jigawa, Nasarawa, Plateau da kuma jihar Abia ne ke Karar Shugaban Kasa da Gwamnatin Tarayya
  • Sun dai Nemi Babbar Kotun ne ta Cire Dokar da Muhammadu Buhari Yasa Ta 16 ga watan Fabrairu na cewar, ₦200 kawai Za'a Dawo a Cigaba da Amfani da ita Banda Sauran Kudaden.
  • Matsalar Dokar Tasa A Abuja, masu sana'ar POS Suna Daukarwa Mutane N300 akan N1,000; N1,500 akan N5,000; N1,800 akan N6,000; N2,100 akan N7,000; N3,000 akan N10,000, N6,000 akan N20,000 , N40,000 akan N100,000.

A kwanakin baya ne dai Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sake fasalin kuɗi tare da rage musu yawan zirga-zirga.

A cewar fadar ta Villa, sunyi haka ne ba don komai ba face sai don tabbatar da anyi zaɓe sahihi, kuma an rage yanayin yadda ake amfani da kuɗi wajen sojan ƙuria.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Ɓarayi 50 da Suka Sace Kaya a Gobarar Kasuwar Maiduguri.

A yau ne ake sa ran babban bankin Najeriya zai kawo karshen taƙaddamar da ake ta fama akan canja fasalin na ƙudi.

Sample
Yau Take Ranar Yanke Hukunci Akan Canja Fasalin Naira Da Hana Kudi Zurga-Zurga Photo: premiumtimesng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan kafa kwamiti na alƙalai da akayi guda bakwai domin su saurari ƙarar tare da kuma umartar waɗanda suke ƙara su 17 domin su tattara hujjojin su.

Masu ƙarar sun haɗa da Kaduna, Kogi, Zamfara, Katsina, Lagos, Cross River, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Rivers, Kano, Niger, Jigawa, Nasarawa, Plateau da kuma jihar Abia.

Masu kare kan nasu sun haɗa da Gwamnatin tarayya, jihar Edo da kuma Bayelsa.

Kowacce jiha ta shigar da ƙara ne akan rashin sahihancin dokar a shariance, sannan jihohin sun buƙaci da a cire dokar ta dawo babu ita, inda aka dunƙule su domin saurarar su bai ɗaya.

Babban Lawyan jihar Zamfara, Abiodun Owonikoko ya nemi da babbar kotun ta cire dokar ta Muhammadu Buhari ga 16 ga watan Fabrairu na cewar, ₦200 kawai za'a dawo a cigaba da amfani da ita.

Kara karanta wannan

Yan Watanni Bayan Rabuwa Da Matarsa Da Kuma Musulunta, JJC Skillz Yayi Aure A Kano

Owonikoko, wanda yake gangaran ɓangaren lawyanci (SAN) ya ƙara da cewa, canja fasalin Naira ya saɓa da sashe na 17(2)(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda yace ayyukan gwamnati dole ne su kasance suna jiɓantar rayuwar ƴan adam.

Amma wasu gungun gangaran a fagen lawyanci (SAN), Agabi (SAN), Tijani Gazali (SAN), Kenneth Mozia (SAN) da Audu Anuga (SAN) waɗanda suke wakiltar masu ƙara sunce, ya kamata kotun ta kori shari'ar saboda rashin iya aiki na masu kariya.

Kamar yadda Agabi ya kafa hujja da cewar, waɗanda ya kamata suzo gaban kotun basu bane a gabanta, domin sun gaza haɗawa da shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a ciki.

Ya tabbatar da cewa, aƙalla an yi tsokaci sau kusan 32 akan Babban Bankin Najeriya na daga korafin da ake masa , kuma a ƙalla bankin daya sassauto da aƙalla dokoki bakwai, kuma ba'a zayyana buƙatar hakan ba a cikin korafin.

Agabi ya kuma ce, waɗanda yake wakilta a kotun sun shigar da ƙorafi ne suna fatan ganin an daina amfani da fom mai lamba 48 wanda aka shigar da babban lauyan gwamnati (AGF) da Emefiele, inda yace kundin na shari'ar ya nuna me dalilin da yasa za'ai amfani da Form 47, shima an shigar da ƙarar sa.

Kara karanta wannan

"Tinubu Na Iya Soke Dokar Sauya Fasalin kudin Naira na CBN A Satin Sa Na Farko a Ofis" Masani

Sannan ya jaddada cewar, Buhari bai ƙi bin umarnin kotu ba a wani saƙo daya gabatarwa ƴan ƙasa a ranar Fabrairu ta 16 ga wata, inda yace yin hakan abu ne mai kyau da aka yi wanda yake buƙatar ayi shi lokacin daya dace.

Daga wani ɓarin kuma, akwai alamun sauƙi a al'amuran yau da kullum yayin da ƴan Najeriya suka kama masu sana'ar POS a matsayin wajen da suke zuwa domin samun tsabar kuɗi.

A Abuja, masu sana'ar POS suna ɗaukan N300 akan N1,000; N1,500 akan N5,000; N1,800 akan N6,000; N2,100 akn N7,000; N3,000 akan N10,000, N6,000 akan N20,000 , N40,000 akan N100,000.

Wata mai sana'ar POS wacce ta bada sunan ta a matsayin Edith kawai, tace itama tana ɗaukar kuɗin da aka zayyano a sama, inda tace CBN ne yaja wannan balahirar.

Edith tace, babu sallar kuɗin ko a bankuna, sannan ta ƙalubalanci babban bankin Najeriyar daya saki kuɗi ga bankuna.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

Edith tace taje ta ajiye Naira Miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da wani gidan mai, inda aka bata Naira miliyan ɗaya na zunzurutun kudi na takarda sati uku da suka wuce.

Inda tace, Miliyan 1.2 shi ake bayarwa gidajen mai suke bada Miliyan 1, kuma masu POS dake da zafin nama a shirye suke su biya fiye da haka domin su samu.

Sai tayi raddi mai zafi ga CBN akan yadda suke gallazawa masu POS, inda ta musanta da cewa, duk mai son kuɗi tsaba, dole ne ya biya ya amsa.

A cewar ta:

" CBN bai san nawa muke biya ba domin samun tsabar kuɗi ba. Inda ace akwai tsabar kudi daga CBN, bazamu kasance cikin wannan satokasakatsin ba. Kada aga laifin masu POS, a zargi CBN."

Yayin da majiyar mu ta The Nation ta ziyarci yawancin bankunan dake cikin birane, yawancin su basu da tsabar kuɗi a wajen amsa da ajiye kuɗi ballantana injinan bada kuɗi na ATM.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Obi Atiku? INEC Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zabe a Kogi

A Lagos, wani mai POS a Eleko da ake kira da Roseline Okon, tace tana sayo zallar kuɗi tsaba ne a manya manyan kasuwanni na Super market, gidan mai, da kuma mutane ɗaiɗaiku da suke da zallar kuɗin mai yawa.

" Kungiya ta tana zuwa manya manyan kasuwanni ne neman mai zallar kuɗi. Muna biyan 11,000 abamu 10,000 ne. Waɗanda suka zo wajen mu neman kuɗi kuma, muna basu 6500 ne akan 5000 na transifa.

Ɗaya daga cikin masu amsar tsabar kuɗi Michael Adigun, yace ya yanke hukuncin ɗiyan kuɗi tsaba ne saboda matsalar netiwok.

A cewar sa:

" Ban taɓa tunanin zan sayi zallar kuɗi ba. Amma ba dama sai dai nayi hakan, saboda na tura kuɗi yaki zuwa. na bada 6500 an bani 5000 saboda in warware wasu buƙatun ujila da suka taso min. Inji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida