Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa

Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa

  • Shugabannin kasashen duniya na cigaba da aiko da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, kan nasararsa a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Na baya-bayan cikinsu shine Mai Martaba Sarki Mohammed VI na kasar Morocco wanda ya ce yana yi wa tsohon gwamnan na jihar Legas fatan nasara da alheri a ofis
  • Sarki Mohammed ya kara da cewa yana fatan yin aiki tare da gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu domin karfafa dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu tare da aiwatar da ayyuka da za su amfane kasashen biyu

Morocco - Sarkin Kasar Morocco, Sarki Mohammed VI, ya taya zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu murnar nasararsa a zaben ranar Asabar da ta gabata, Daily Trust ta rahoto.

Tinubu ya yi nasarar lashe zaben ne da kuri'u fiye da miliyan takwas a cewar alkalluman da hukumar INEC ta fitar sai Atiku Abubakar na PDP ke biye da shi.

Kara karanta wannan

2023: "Ban San Komai Ba" Atiku Ya Maida Martani Kan Yunkurin Tinubu Na Neman Sulhu

Sarki Mohammed VI
Sarki Mohammed VI na Morocco ya taya Tinubu murnar cin zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sarkin ya yi wa Tinubu fatan nasara a ofis, yayin da ya ke taya shi murna.

Ya ce:

"Domin amincewar da al'ummarsa suka yi masa, domin cimma burinsu na samun karin cigaba da wadata."

Sarki Mohammed ya ce yana fatan karfafa zumuncin da ke tsakanin Najeriya da Morocco karkashin gwamnatin Bola Tinubu.

Sanarwar ta kara da cewa:

"A wannan lokacin, Sarki na nuna gamsuwarsa da alakar yan uwantaka na Afirka, hadin gwiwa mai ma'ana da hadin kai tsakanin Morocco da Najeriya, da kudirinsa na aiki tare da Bola Tinubu don karfafa kawance tsakanin kasashen biyu, fadada hadin gwiwar a sabbin bangarori da za su amfana mutanen kasashen biyu, da ba da gudummawa ga ci gaba, kwanciyar hankali da hadin kan nahiyar Afirka."

Kasar Amurka ta aika wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sakon taya murna kan nasarar lashe zaben shugaban kasa

Kara karanta wannan

2023: "Ta Tabbata Tinubu Ne Zabin Yan Najeriya" Shugaban APC Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

A ranar Laraba 1 ga watan Maris, kasar Amurka ta mika sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Ned Price, mai magana da yawun ma'aikatan harkokin kasashen Amurka ne ya fitar da takardar taya murnar a madadin kasarsa.

Ya ce:

"Amurka na taya yan Najeriya da zababben shugaban kasa Bola Tinubu da shuwagabannin siyasa murna."

Har wa yau, Amurka ta yi kira ga sauran yan kasar su zauna lafiya sannan wadanda suke ganin an yi musu ba daidai ba su bi tsarin doka su tafi kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164