Yan Bindiga Sun Yi Wa Samanja Kisar Gilla A Cikin Gonarsa A Neja
- Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun tafi gona sun halaka wani mutum dan shekara 52 mai suna Samanja a garin Baje-Patiko, Jihar Neja
- Watar yar uwar Samanja, Easter Barde, ya ce marigayin ya tafi gonarsa ne da safiyar ranar Talata domin ya shuka kubewa sai yan bindigan suka harbe shi
- Barde ta kara da cewa mafi yawancin mutanen garin Baje-Patiko da ke karamar hukumar Manya sun yi hijira zuwa Sarkin-Pawa saboda tsoron harin yan bindiga
Jihar Neja - Yan bindiga sun harbi wani manomi dan shekara 52 da aka ce sunansa Samanja, a Baje-Patiko karamar hukumar Munya ta jihar Neja, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wani dan uwan marigayin, mai suna Easter Barde, ta fada wa City & Crime cewa an bindige Samanja ne a wuyansa yayin da ya ke aiki a gonarsa a safiyar ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Easter Barde ta yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe Samanja
Ta bada bayani cewa:
"Saboda yawan hare-hare da ake kawo wa yankin, mazauna mafi yawancin kauyukan da ke yankin sun bar gidajensu suna zaune a matsayin yan gudun hijira a Sarkin-Pawa, hedkwatar karamar hukumar Munya.
"Don haka, daga Sarkin-Pawa ne Samanja ke zuwa gonarsa a kullum. Ya tafi gonar ya shuka kubewa a safiyar ranar Talata kuma yan bindigan suka tarar da shi a can suka kashe shi."
Ta ce Samanja, wanda ya rasu ya bar dattijon mahaifinsa, shine kadai dan mahaifinsa da ya rage.
A cewarta, sai da aka dangana da yan banga na yankin kafin aka kwato gawar marigayin daga gona.
Yan bindiga sun halaka mai sarautar gargajiya, sun kuma sace wasu mutum 3 a jihar Neja
A wani rahoton kun ji cewa wasu yan fashin daji sun kai mummunan hari a karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja inda suka kashe Magajin Garin kauyen Mulo sannan suka yi awon gaba da mutane uku.
Kamar yadda Vanguard ta rahoto, yan ta'addan sun yi wa basaraken, Alh. Usman Garba, kisa mai muni sannan suka jefar da gawarsa a kan hanya, suka kuma tafi da sauran mutanen uku.
Emmanuel Umar, kwamishinan harkokin jin kai da tsaron cikin gida na jihar Neja ya tabbatar da afkuwar harin a wata hira da ya yi da manema labarai a gidan gwamnatin Neja.
Asali: Legit.ng