Masu Garkuwa da Matata Sun Nemi Na Siyar da Motata Na Haɗa Masu 8m, Basarake

Masu Garkuwa da Matata Sun Nemi Na Siyar da Motata Na Haɗa Masu 8m, Basarake

  • Basaraken Bukpe a yankin Abuja, mai martaba Alhaji Hassan Shamdozhi, ya faɗi halin da ake ciki game da garkuwa da iyalinsa
  • Ya ce masu garkuwa sun nemi ya haɗa masu miliyan N8m kuɗin fansa kuma sun nemi ya sayar da motarsa
  • Tun a farkon watan Fabrairun da ya gabata, maharan suka je har gida suka sace matarsa da 'ya'yansa maza 2

Abuja - Basaraken gargajiya na Bukpe da ke yankin ƙaramar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja, HRH Alhaji Hassan Shamdozhi, ya bayyana sakon da masu garkuwa suka aiko masa.

Basaraken, mai martaba a yankinsa ya ce 'yan bindigan da suka yi garkuwa da matarsa sun aiko masa da sakon ya siyar da motarsa ta hawa ya haɗa musu miliyan N8m kuɗin fansa.

Matsalar garkuwa da mutane.
Masu Garkuwa da Matata Sun Nemi Na Siyar da Motata Na Haɗa Masu 8m, Basarake Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A ranar 4 ga watan Fabrairu, 2023, masu garkuwa suka kutsa gidan Sarkin suka yi awon gaba da ɗaya daga cikin matansa, Sadiya Hassan Shamdozhi tare da 'ya'yansa maza 2.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe, Babban Jigon PDP Ya Jingine Tafiyar Atiku, Ya Koma Jam'iyyar APC

Da yake zantawa da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho ranar Laraba, Basaraken ya ce ya shiga matsanancin yanayi game da batun garkuwa da matarsa da yaransa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce masu garkuwan sun tuntube shi ranar Talata ta hannun ɗaya daga cikin 'yan uwansa, sun umarci ya sayar da motarsa ta hawa domin ya harhaɗa kudin da suka nema fansa.

A kalamansa, Mai martaba Alhaji Hassan Shamdozhi ya ce:

"Maganar gaskiya na shiga ruɗani, gobe Alhamis wata ɗaya kenan da sace matata da 'ya'yana biyu. Lokacin da suka kira jiya Talata, sun faɗamun na siyar da motata na haɗa miliyan N8m kafin su sake su."
"Da farko sun nemi miliyan N3m, ba zato suka sauya tunani suka koma miliyan N8m, sun ce ko motata na siyar na haɗa kuɗin. Ko da na sayar da motar ba zata wuce miliyan ɗaya ba."

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Peter Obi Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Ci Zabe, Ya Yi Alkawarin Abu 1 Tak

Daga nan ya yi kira da hukumomin tsaro da su tausaya masa, su yi duk ne yuwuwa wajen kubutar da iyalansa cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Har zuwa yanzun, kakakin rundunar yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta tabbatar da batun neman kuɗin fansa ba.

'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 a Enugu

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi ajalin ɗan takarar Sanata na jam'iyar Labour Party a zaben 2023 a jihar Enugu

Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce bayan maharan sun bindige shi har lahira tare da wasu mutum biyar, sun cinna wa gawarsu wuta.

Lamarin dai ya ta da hankulan mutane da dama a yankin a daidai lokacin da ake cikin harkokin zaɓe a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262