Gaskiya Ta Bayyana Kan Kisan Ɗan Gwamnan Rivers a Ƙasar Waje
- Labarin da ake yaɗawa cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya rasa yaron sa a ƙasar Amurka ba gaskiya bane
- Wani rubutu da ya yaɗu a soshiyal midiya yayi iƙirarin cewa an bindige ɗan gwamnan a ƙasar Amurka bisa sa hannun ayi maguɗin zaɓe a jihar Rivers
- Sai dai kwamishinan watsa labarai na jihar ya fito ya raba tsakanin aya da tsakuwa inda ya tabbatar da cewa babu wani ahalin gwamnan da yake rayuwa a ƙasar Amurka
Jihar Rivers- Rahoton da ke cewa Jordon Nyesom, ɗan gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, an bindige shi har lahira a ƙasar Amurka, ba gaskiya bane.
PM News ta rahoto cewa wani rubutu da ya karaɗe soshiyal midiya ya nuna cewa an halaka ɗan gwamna Wike a ƙasar Amurka kan zargin yana da hannu wajen yin maguɗi a zaɓen ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, na shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya, a jihar Rivers.
A kwanakin baya hotunan Jordan Nyesom lokacin kammala karatun sa a jami'ar Exeter ta ƙasar Ingila sun bayyana a watan Yuli.
A tare da shi akwai mahaifin sa, gwamna Wike tare da matar sa Jostis Suzette da ɗiyar su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ba gaskiya bane
Da yake martani kan rahoton kisan ɗan gwamnan, kwamishinan watsa labarai na jihar Rivers, Chris Finebone, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Maris, ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamna Wike baya da wani ɗa ko ɗiya a wanda yake rayuwa a ƙasar Amurka.
A cewar Finebone, rahoton aikin wasu mugayen mutane ne waɗanda ke ɓata sunan gwamnan Wike sannan ya nemi al'umma da suyi watsi da wannan labarin na ƙarya.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
“Wannan wata tsantsagwaron ƙarya ce da wasu mugayen mutane suka shirya. Domin kayar da dukkanin wani shakku, gwamna Wike baya da ɗa ko yaro a ƙasar Amurka."
"Da yardar Allah, ƴaƴan gwamnan suna cikin ƙoshin lafiya a duk inda suke."
Kotu Ta Tasa Keyar Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai Zuwa Magarkama
A wani rahoton ƴan sanda sun tasa ƙeyar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, zuwa magarƙama.
Shugaban masu rinjayen na majalisar yana fuskantar tuhume-tuhume da dama a kansa.
Asali: Legit.ng