Bola Tinubu Ya Kafa Kwamitin Sulhu Don Ganawa da Peter Obi da Atiku Abubakar, Inji Akeredolu
- Gwamnan jihar Ondo ya bayyana shirin Bola Ahmad Tinubu kan sauran ‘yan takarar da ya buga da kasa a zaben bana
- Gwamnan ya ce, Tinubu ya kafa kwamitoci domin ganawa da su Atiku da Obi don dinke barakar da ka iya tasowa a gaba
- An yi zabe a Najeriya, Tinubu ya fi dukkan ‘yan takarar tara yawan kuri’u, wasu ‘yan takara sun bayyana rashin amincewar
FCT, Abuja - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bayyana cewa, zababben shugaban kasan Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kafa wani kwamitin sulhu bayan lashe zaben 2023.
Gwamnan ya ce, kwamitin zai zauna ne da sauran ‘yan takarar da suka fafata da Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Faburairu domin yin sulhu da su.
A cewarsa, kwamitin zai hada da manya kuma dattawan jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Gwamna Rotimi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja a lokacin da INEC ta ba Tinubu takardan shaidan lashe zaben bana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda zaben bana ya kasance
A zaben na bana, Tinubu ne ya samu yawan kuri’un da 8,794,726, Atiku ya samu 6,984,520 sai kuma Peter Obi mai kuri’u 6,101,533.
A wata sanarwar da Richard Olatunde, sakataren yada labarai na gwamna Rotimi ya fitar, ya ce wannan zaben ya yi daidai da muradin masu kada kuri’u, Daily Post ta ruwaito.
Sannan, gwamnan ya ce duk wani dan takarar da bai ji dadin sakamakon ba, za a zauna dashi domin yin sulhu.
A kalamansa:
“Zababben shugaban kasan ya kafa kwamitoci don ganawa da ‘yan takarar da suka fafata a zaben domin a fara duba hanyar warkar da lamura.
“Ni ina cikin daya daga cikin kwamitocin. Za mu gana dasu kuma mu roke su da su yi aiki tare da mu.
An ba Tinubu shaidar shi ya lashe zaben bana
A tun farko kunji cewa, hukumar zabe ta INEC ta kira Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima domin ba su shaidar lashe zabe a bana.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da Farfesa Mahmud Yakubu ya ayyana Tinubun a matsayin wanda ya lashen shugaban kasa a Najeriya.
Bayan taron, Tinubu ya yi maganganu masu daukar hankali game da shirinsa ga kasa Najeriya.
Asali: Legit.ng