Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Ekiti Fayose, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Ekiti Fayose, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

  • Fayose Yace Ya Bayyana Dalilai Da Suka Gaza Kai PDP Nasara inda ya bayyana asalin Matsalar PDP
  • Inda Yace Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar PDP Atiku Abubakar daya gaza samun daidaito da gwamnonin jam'iyyar na G-5
  • Fayose Yace Nasarar da Peter Obi yayi a Legas, ya nunawa Mutane cewar Zaɓen da Akayi babu wani magu-magu saboda haka kowa ya kamata ya Amshi Sakamakon haka.

Legas - Yayin da aka kammala sanin wanda yayi nasara a zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun dokokin da tarayya. Mutane na ci gaba da bayyana matsayar su da ra'ayin su dangane da zaɓen mai cike da cece kuce.

Hakan ce tasa Fayose, tsohon gwamna a Ekiti, ya bayyana wani abu daya girgiza magoya bayan jam'iyyar PDP kwata.

Fayose, ya bayyana cewar daga rana irin ta yau, shi ba ɗan jam'iyyar PDP bane. Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a matsayin baƙo a wani shiri da ake gabatarwa mai taken ARISE News.

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

Ayodele Fayose
Ayodele Fayose Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan za'a iya tunawa dai, Fayose yayi gwabna daga shekarar 2003 zuwa 2007 sannan ya sake yiwa Ekiti gwabna daga shekarar 2011 zuwa 2015 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Masu sharhi akan al'amuran siyasa na ganin ficewar sa daga PDP nada alaƙa mai ƙarfi da rashin jituwa dake a cikin jam'iyyar ta PDP wanda yake ganin ɓarakar bazata ɗinku ba.

A cewar Fayose:

"Bara na jaddada wannan batu nan, daga rana irin ta yau (jiya) Na fice daga jam'iyyar PDP. A siyasar cikin gida ta jam'iyyu, akwai abubuwan da bazaka taɓa magana akai ba. Shekaruna 62, a waɗannan shekaru bazan zo ina zabga ƙarya ba. Idan kana da matsalar yali ka bayyana."

Tsohon gwamnan da yayi iƙirarin yayi wa jam'iyyar yaƙi da jinin sa da gumin sa, yace PDP ta gaza samun nasara ne a zaɓen daya gabata saboda matsalar shugabanci da take fama dashi.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Yace jam'iyyar PDP a karairaye take tun kafin zaɓen shugaban ƙasan daya gabata.

Wacce take ɗauke da fushin yan takarkaru da shugabancin jam'iyyar ya gaza yiwa adalci, musamman ma yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya gaza samun daidaito da gwamnonin G-5.

Fayose yace, asalin matsalar PDP ta samo asali ne a taron Arewa-Maso Yamma wanda akayiwa Rabiu Kwankwaso maguɗi saboda Tambuwal, wanda hakan yasa Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar.

Fayose ya ƙara da cewa:

"Na gargaɗi Atiku akan matsalar data dilmiyar da PDP. Nace masa, akwai matsala anan gaba. Nace da Atiku yayi sanarwa a hukumance, ya rabawa manema labarai cewar zaiyi mulki shakaru huɗu ne kawai sai ya bawa ko waye a kudu, amma ina Ayu yaƙi bari ayi hakan".

Ya gargaɗi Obi daya fice daga jam'iyyar PDP, sannan yace da ace PDP sun yarda da nagartar Obi dashi suka bawa takara, Fayose ya kuma sarawa Obi akan yadda ya bawa mara ɗa kunya.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Zai Kasance Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello

Ya bayyana Obi a matsayin abun ban mamaki, kuma mai lokaci. Inda yace nasarar Obi a Lagos ya nuna abubuwa sun soma sauyawa a siyasance.

Thisday ta ruwaito Fayose yana cewa, nasarar da Peter Obi yayi a Legas, ya nunawa mutane cewar zaɓen da akayi babu wani magu-magu saboda haka kowa ya kamata ya amshi sakamakon haka.

Fayose ya kuma alakanta nasarar zaɓen da yin amfani da na'urar BVAS wanda yace itace take da alhakin kawo adadin mutane daga ko ina na ƙasar nan, adadi kuma wanda hankali zai iya amsa.

Ya kuma ƙare da cewa, duk masu cewa a soke zaɓen da akayi, yace ba wani abu suke ba face kwangilar da jam'iyyar PDP ta basu suyi.

Gwamna Masari Ya Tattauna Da Buhari Kan Zaben Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnan na Jihar Katsina ya ce ya je don taya shugaba Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa da jam'iyyar APC tayi.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kashi a Zaɓe, Sanatan NNPP Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa PDP a Jihar Bauchi

Masari ya kuma bayyana cewa Buhari yafi kowa farin ciki ganin yadda APC ta lashe zabe saboda zai mika mulki ga dan jam'iyyar sa.

Aminu Masari ya bayyana abin da suka tattauna da shugaba Buhari wa yan jarida bayan kammala ganawar sirri da shugaban kasar mai barin gado

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida