Bayan Ya Sha Kashi a Zaben Sanata, EFCC Ta Samu Damar Ram da Jigon APC a Kano
- Abdulsalam Saleh Abdulkarim Zaura ya shiga hannun Hukumar EFCC, har an shiga da kararsa a kotu
- EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa tayi kararsa a kotun tarayya a Kano
- Ishaq Mudi Dikko (SAN) ya yi nasarar karbo belin A. A Zaura a hannun Alkali Mohammed Nasir Yunusa
Kano - Bayan tsawon lokaci ana nemansa, Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa watau EFCC ta yi nasarar cafke A. A Zaura.
Hukumar EFCC ta fitar da jawabi a shafinta a yammacin Laraba, ta tabbatar da cewa an gurfanar da Abdulsalam Saleh Abdulkarim Zaura a kotun tarayya.
Jami’an hukumar kasar sun maka Attajirin ‘dan siyasar ne a gaban Alkali Mohammed Nasir Yunusa na babban kotun tarayya mai zama a garin Kano.
Ana tuhumar jigon na jam’iyyar APC a Kano da aka fi sani da A. A Zaura da aikata laifuffuka hudu.
Zargin da ke kan A. A Zaura
Zargin da ke kan wuyan Zaura sun hada da fakewa da sunan wani, karbar Dala $200, 000 a hannun Dr. Jamman Al- Azmi a shekarar 2014 ta hanyar zamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyoyin EFCC su na tuhumar wannan mutum da yin gaba da kudin Jamman Al- Azmi a garin Kano da sunan za su hada-kai domin yin harkar kasuwanci.
'Ban aikata laifi ba' - Zaura
Da Lauyar EFCC, Aisha Tahar Habib ta jero masa laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa, ‘dan siyasar ya nuna bai san da zaman wadannan laifi ba.
Ishaq Mudi Dikko (SAN) wanda yake kare wanda ake kara, ya bukaci Alkali ya bada belin A. A Zaura, kuma aka yi nasara Mai shari’a ya amince da hakan.
BBC Hausa ta ce an dakatar da shari’ar sai zuwa ranar 2 ga watan Mayu 2023 sannan Alkali Mohammed Nasir Yunusa zai fara sauraron Lauyoyin bangarorin.
Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya dade yana fuskantar kara daga hukuma a gaban kotu.
Sahara Reporters ta ce za a sake yin shari’a da ‘dan takaran APC na Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023 ne bayan babbar kotu ta soke wanke shi da aka yi.
Za a shiga kotun karar zabe
Labari ya zo cewa Sanata Dino Melaye ya ce babu ja da baya a kan batun zuwa kotun zabe domin soke nasarar APC, PDP ta na ganin ita ta lashe zaben bana.
A madadin Peter Obi, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya nuna LP za ta nemi hakkinta ta hanyar shari'a, 'dan takaran ya nuna an tafka murdiya da magudi.
Asali: Legit.ng