Kotu Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Wata 6 a Gidan Kaso Bisa Satar Fankoki
- Wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kano ta tura wani matashi mai halin ɓera zuwa gidan gyaran hali
- Alƙalin kotun ya kuma bayar da umurnin a bulale matashin saboda wannan gagarumar satar da ya tafka
- Matashin ya dai lallaɓa wata babbar kwaleji ne a jihar inda yayi awon gaba da tarin wasu fankoki
Wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kano, ta yanke wa wani matashi mai suna Murtala Halliru, mai shekara 20 a duniya, hukuncin wata shida a gidan gyaran hali.
Kotun ta tura Murtala gidan gyaran hali na wata shida da bayar da umurnin ayi masa bulali 30, bisa satar fankoki 13. Rahoton The Punch
Matashin wanda yake rayuwa a Gwammaja 'Quarters' a Kano, an yanke masa hukunci ne bayan ya amsa tuhumar da ake masa.
Alƙali mai shari'a, Nura Yusuf-Ahmad,he presiding Judge, Nura Yusuf-Ahmad, ya yanke masa hukuncin zama a gidan gyaran hali na tsawon wata shida ba tare da zaɓin biyan fansa ba, sannan ya bayar da umurnin a yi masa bulala 30.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alƙalin ya kuma umurce matashin da ya biya N44,000 a matsayin kuɗin fansar fankokin da ya sace. Rahoton The street Journal
Tun da farko, lauya mai shigar da ƙara, Aliyu Abideen, ya gayawa kotun cewa wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Fabrairu a Kwalejin kimiyya ta Kano.
Yace kuma a ranar ne aka cafke wanda ake zargin ɗauke da fankokin a bayan keken sa wanda kuɗin su ya kai N8,000.
“A yayin da ake gudanar da bincike, wanda ake ƙarar ya amsa cewa ya saci fankoki 11 wanda kuɗin su ya kai N44,000, a makarantar." A cewar Abideen
Ya kuma ƙara da cewa, laifin ya saɓawa sashi na 133 na dokar shari'ar musulunci ta jihar Kano.
EFCC Ta Kama Malamin Jami'ar Najeriya Da Tsabar Kudi N306k A Rumfar Zabe
A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC ta cafke wani malamin jami'a da maƙudan kuɗaɗe a rumfar zaɓe.
Jami'an hukumar masu sanya ido kan zaɓe sune suka yi caraf da lakcaran. a ranar zaɓe.
Asali: Legit.ng